Follow Us @soratemplates

Sunday, October 8, 2017

Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna

Ana zargin wani jamiā€™in dan sanda a jihar Kaduna da harbin wata budurwa saboda taki amince da soyayyarsa
- Buduruwar ta kasance daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja
- Shaā€™awa ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya harbe ta
Ana zargin wani jami'in dan sanda a Kaduna da harbin wata budurwa da bindiga saboda taki amincewa da soyayyarsa.
Majiyar bestarewa.com.ng
 ta ruwaito budurwar mai suna Shaā€™awa Nasiru, mai kimanin shekaru 20 da haihuwa daga kauyen Gadar Mallam mamman dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Majiyar ta bayyana cewa dan sandan ya labe ne a lokacin da ya hangi shaā€™awa ta shiga wani gida, yayin da take fitowa sai ya kira sunanta, tana amsawa zai ya saka mata harsashi.

KarkYi share wannan
Soyayya: Wani dan sanda ya harbe wata budurwa saboda taki amsa soyayyarsa a Kaduna
Budurwar da aka harbe a kan so

KarkYi share wannan
Nan da nan mutane suka watse a guje sakamakon jin harbin bindigar kafin daga bisani wasu suka garzaya inda budurwar take a kwance cikin jini suka dauke ta zuwa asibitin Doka dake jihar Kaduna, amma abin yafi karfinsu, inda suka ce a mika ta zuwa babban asibiti, sai dai hakan bata samu ba sabida yajin aikin da kungiyoyin maā€™aikatan lafiya suke yi, ciki kuwa har da asibitin koyarwa dake Gwagwalada.

KarkYi share wannan
Wata kawar ta mai suna Salamatu Sani ce ta shaidawa wa majiyar mu cewa, ā€œShaā€™awa ta shaida wanda ya harbe ta a lokacin da suka iso wajenta cikin gaggawa, a inda ta shaida cewar ā€˜insfekto ne' ", inji kawar ta.

KarkYi share wannan
Sai dai duk yunkurin da majiyar tamu tayi don jin ta bakin kakakin rundunar ā€˜yan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu abun yaci tura domin yaki amsa kiran kuma yaki maido da sakon tes da akayi masa kan batun.

KarkYi share wannan

No comments:

Post a Comment