Follow Us @soratemplates

Showing posts with label Siyasa. Show all posts
Showing posts with label Siyasa. Show all posts

Wednesday, April 25, 2018

Siyasa Nigeria : Su waye za su ja da Buhari a zaben 2019?

April 25, 2018 0 Comments
Kodayake Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 ba, amma na kusa da shi sun sha bayyana cewa babu abin da zai hana shi yin tazarce.
A watan Mayun shekarar 2015 ne Shugaba Buhari ya yi rantsuwar fara mulkin wa'adin shekara hudu karkashin jam'iyyar APC, kuma yana da damar sake neman wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.
Sai dai akwai wadanda suke ganin bai kamata shugaban ya nemi tazarce ba, ciki har da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Mun yi nazari kan mutanen da ake ganin za su iya kawar da Shugaba Muhammadu Buhari daga kan mulki a zabe mai zuwa?
Sanata Bukola Saraki
Mutum na biyu cikin manyan 'yan siyasar kasar wanda ake ganin watakila ya nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya shi ne Shugaban Majalisar Wakilai Sanata Bukola Saraki.
Kodayake a halin yanzu ya musanta hakan, amma a baya sau biyu yana neman tsayawa takarar shugabancin kasar.
Sai dai wadansu suna ganin da wuya Sanata Saraki ya iya samun tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyarsa ta APC, musamman ma idan Shugaba Buhari zai yi takara.
Amma dai yana da alaka da 'yan siyasa, ga kudi, ga kuma kwarewa a siyasance.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Har ila yau, a zauren majalisar dattawan kasar, akwai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ma ya taba neman shugabancin kasar a 2015 amma Buhari ya kayar da shi a zaben cikin gida a APC.
Kodayake a wannan karon bai bayyana aniyyarsa ba tukunna, amma alamu na nuna cewa har yanzu bai hakura ba, kuma watakila ya kara gwada sa'arsa.
Tsohon gwamnan jihar Kanon shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na 'yan takarara neman shugabancin a jam'iyyar APC a zaben 2015.
Masana suna ganin a wannan karon, zai iya samun tikitin shugabancin kasa a jam'iyyar musamman idan Shugaba Buhari ya ki amincewa ya sake yin takara.
Alhaji Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yana daya daga cikin mutanen da ake ganin za su sake gwada sa'arsu, bayan ya nemi zama shugaban kasar har sau uku a baya.
Akwai wadanda suke ganin sha'awarsa ta zama shugaban Najeriya ce ta sa ya koma jam'iyyar PDP daga jam'iyyar APC mai mulki a watan Disambar bara.
Ga dukkan alamu Alhaji Atiku Abubakar yana ganin zai fi samu damar kara gwada sa'arsa a jam'iyyar PDP.
Sai dai wasu na ganin ba lallai ne jam'iyyar ta ba shi tikitinta ba.
Ayodele Fayose
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose shi ne wanda ya fara bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP.
Gwamnan Fayose wanda an riga an fara yada hotunan kamfe dinsa a fadin kasar, mutum ne da ke yawan nuna adawarsa ga jam'iyyar APC da kuma Shugaba Buhari.
Gwamnoni suna da matukar tasiri a siyasar Najeriya, abin da ya sa wadansu masana suke ganin kila shi ya sa Mista Fayose yake kokarin ganin ya gwada sa'arsa.
Alhaji Sule Lamido
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa yana daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya da ake ganin watakila shi ma ya nemi takarar shugabancin kasar a zaben 2019.
Sai dai shi ma bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta yin hakan ba tukunna.
Alhaji Sule Lamido yana daya daga cikin wadanda suke sukar gwamnatin APC da Shugaba Buhari.
Shin 'yan majalisa na shirin yi wa Buhari wayo a zaben 2019 ne?
Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 - Malami
2019: Ministar Buhari 'ta fara yi wa Atiku kamfe'
Malam Jafar Jafar wani mai sharhi ne kan harkokin siyasar Najeriya, kuma ya ce yana ganin duk wani dan siyasa da yake neman takara a jam'iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne kawai, "matukar Shugaba Buhari zai sake yin takara."
Ya ce: "Idan har Buhari zai yi takara, to babu makawa jam'iyyarsa shi za ta tsayar a zaben 2019."
"Kuma da wahala a ce ba zai yi takara ba," in ji shi.
Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu muradin yin takara a jam'iyyar APC shi ne kawai su sauya jam'iyya.
"Ga jam'iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta iya faduwa zabe."
"Saboda a gaskiya farin jinin jam'iyyar da na Shugaba Buhari ya ragu sosai."
Mai fashin bakin ya ce abin da ya sa manyan 'yan siyasar kasar ba su fito sun bayyana aniyarsu ta takara ba, "shi ne kamar wata dabara ce suke don su fito tashi guda idan lokacin fara yakin neman zabe ya yi."
'Yan kasar dai sun zuba ido su ga jerin mutanen da za su fito su bayyana aniyarsu ta neman kuri'unsu

Siyasa Nigeria : Me ya sa Atiku ke son shugabancin Najeriya?

April 25, 2018 0 Comments
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce akwai dalilai da dama da suka sa ya dawo daga rakiyar Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Jimeh Saleh bayan wata ziyara da ya kai ofishin BBC da ke Landan ranar Litinin.
A watan Disamabar bara ne Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC, inda daga bisani ya koma jam'iyyar hamayya ta PDP.
Ya ce "bayan da Shugaba Buhari ya kama mulki jam'iyyar APC ta fara tafiya ne a gurgunce."
"Sannan yadda ake gudanar da gwamnati. Na ba da nawa ra'ayi da wanda na ga kamar ba su da amfani (a wurinsu)."
Atiku ya kalubalanci masu cewa ya yi sata su ba da hujja
Su waye za su ja da Buhari a zaben 2019?
Buhari ya mayar wa Atiku martani
Har ila yau ya ce yana so ya tsaya takarar shugabancin kasar ne saboda ya gyara abubuwan da bai iya gyarawa ba a tsawon shekara takwas da ya yi a matsayin mataimakin shugaban kasar.
"Ina neman shugabancin Najeriya saboda abubuwan da ban iya yi ba don ina mataimakin shugaban kasa, zan samu dama na yi su," in ji shi.
Fitaccen dan siyasar ya ce zai fara ne da gyara tattalin arzikin kasar, idan ya samu nasarar zama shugaban kasar.
Atiku Abubakar ya ce yana da tabbacin 'yan kasar za su yi na'am da shi ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ba da misali da yadda gwamnatinsu ta kafa hukumar EFCC.
'Neman mulki ruwa-a-jallo'
Har ila yau ya ce babu wani da bai zai bincika ba idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Sai dai ya musanta batun da wadansu suke yi cewa idonsa ya rufe wajen neman shugabancin Najeriya.
Hakazalika ya yi karin haske kan batun hana shi izinin shiga kasar Amurka, inda ya ce ya nemi bizar shiga kasar, "amma sun hana ni."
Sai dai da aka tambaye shi dalilin hana shi bizar ta shiga Amurka ya ce shi ma ba a gaya masa dalili ba.
Alhaji Attiku Abubakar ya kuma musanata cewa an yi gwanjon gidansa a Amurka, inda ya ce dama gidan matarsa ne da ya saya mata, kuma "ita ta sayar da kayanta," in ji shi.
Game da kalaman Shugaba Buhari kan matasa na baya-bayan nan, dan siyasar ya ce ra'ayinsa ya sha bamban da na shugaban, "ba na wa matasan kasar kallon cima zaune."
A karshe ya yi kira ga matasan kasar da su shiga harkokin siyasa, inda ya yi alkawarin ba su kaso 40 cikin 100 na ministocinsa idan ya samu nasarar lashe zabe.

Tuesday, April 24, 2018

Siyasar Nigeria : Dino Melaye ya mika kansa ga 'yan sanda

April 24, 2018 0 Comments
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa dan majalisar dattijan kasar mai wakiltar jihar Kogi ta Arewa, Dino Melaye yana hannunta.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya, Aremu Adeniran ya tabbatar wa BBC cewa Sanata Melaye yana hannunsu.
Ya kuma ce shi ne ya mika kansa a safiyar Talata, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter gabanin yin hakan.
Aremu Adeniran ya ce za su ci gaba da tsare Sanata Melaye har sai bayan sun kammala binciken da suke yi a kan zargin da ake yi masa.
A ranar Litinin ne dai 'yan sanda suka yi dirar mikiya a gidan dan majalisar a unguwar Maitama da ke Abuja bayan da jam'ian hukumar shige da fice suka kama shi yayin da yke shirin fita daga Najeriya.
Amma daga bisani an sako shi.
A kwanakin bayan ne rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana dan majalisar dattawan a matsayin wanda suke nema ruwa-a-jallo.
'Yan sandan na zarginsa da kin bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari'a kan zargin daukar nauyin wasu mutane su tayar da hankali da aikata miyagun laifuka.
Sai dai sanatan ya yi watsi da dukkan zarge-zargen yana mai cewa siyasa ce kawai.
An bai wa 'yan sandan duniya umarnin kama Dino Melaye
'Yan sandan Najeriya makaryata ne - Dino Melaye
Sanata Dino Melaye, wanda na hannun damar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne, yana jawo ke-ce-kuce saboda kalamansa na siyasa da kuma salonsa na son rayuwar kasaita.
Dino Melaye a takaice
Dan asalin jihar Kogi, amma an haife shi a Kano
Shekararsa 44
Ya yi karatun firamare a Kano
Ya yi digirinsa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
Yana wakiltar Kogi Ta Yamma a majalisar dattawa
Ya taba zama dan majalisar waklilan Najeriya har sau biyu
An san shi a tarar aradu da ka a harkokin siyasa
Ya taba karbar lamar yabo na dan majalisar wakilan da babu kamarsa daga wata kungiyar matasa
Karin labaran da za ku so ku karanta:
Dino Melaye ya fito a wakar hip-hop
Nigeria: An yi hatsaniya yayin zanga-zangar Dino Melaye

Sunday, October 29, 2017

'Yan PDP ne rabin gwamnatin Buhari – Hameed Ali

October 29, 2017 0 Comments



Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa cika alkawurran da ta yi wa al'ummar kasar na kawo sauyi. Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi lokacin kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar goyon bayan Shugaba Buhari wato (Buhari Support Organisation BSO) a Abuja ranar Juma'a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana. Kungiyar BSO ita ce babbar kungiyar da ta kunshi sauran kungiyoyi da suka shige wa shugaban gaban wajen yakin neman zaben shekarar 2015. "A yanzu, zan iya cewa muna da 'ya'yan jam'iyyar PDP kaso 50 cikin 100 a cikin gwamnatinmu. Ta yaya za a ci gaba da wannan nauyin a kanmu? Ta yaya za mu iya cimma abin da muke fata da wannan nauyin," in ji shi. Ya ci gaba da cewa: "A yanzu 'yan PDP ne suke ba da umarnin abin da za a yi. Wannan ne abin da ya kamata mu yaka.
Za mu yi yaki don kwato hakkinmu da kuma kyawawan manufofin gwamnatinmu." Hakazalika ya ce lokaci ya yi da za su farka daga bacci don samar wa kasar makoma ta gari. Sai dai ya ce "Shugaba Buhari ba shi da wata matsala don yana abin da ya dace ne." Har ila yau ya ce "wadanda suka yi aiki tukuru wajen ganin gwamnatin canji ta kai ga nasara ba a saka musu ba tukuna."
Daga nan ya ce "wajibi ne kungiyar BSO ta tashi tsaye wajen ganin ta jagoranci sabon yakin kawo shugabanci nagari. Dole ne mu yi haka don gyara sunanmu da kuma sunan shugaban kasa da abin da yake yi." "Shugabanmu yana yin abin da ya dace kuma wajibi ne mu ba shi goyon bayan da yake bukata," in ji shi.

Saturday, October 28, 2017

Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice

October 28, 2017 0 Comments
Fitaccen dan majalisar wakillan nan na Najeriya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, 'Yankwashi da kuma Gwiwa dukkan su a jihar Jigawa dake a Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice.
Shahararren dan majalisar dai ya yi wannan caccakar ne a yayin da yake tsokaci a zauren na majalisar game da sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari din da ke fitar da doyar da aka noma zuwa kasashen ketare.
Hausazone.com dai ta samu cewa ta yake tsokacin, Alhaji Gudaji Kazaure ya nuna rashin dubara da kuma sanin ya kamata daga bangaren gwamnatin game da wannan tsarin inda yace shi baiga yadda za'ayi talaka ya mori wannan irin bahagon tsarin ba na fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje sannan kuma an hana shigowa da shi.
Dan majalisar daga karshe sai ya jawo hankanin shugabannin majalisar yan uwansa da ma sauran shugabannin kasar a dukkan matakan mulki da su duba wannan matsala domin kawo gyara.

Saturday, September 30, 2017

Law Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce

September 30, 2017 0 Comments
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin yin shari’ar wasu da ake zargin yan kungiyar nan ce ta Boko Haram ne a asirce ba tare da ba yan jarida damar halartar zaman kotun ba.
Mun samu dai cewa daya daga cikin manyan jami'an ma'aikatar shari'ar kasar ta Najeriya ne dai da bayaso a bayyana sunan sa ya shaidawa kamfanin dillacin labaran kasar Faransa hakan inda kuma ma har ya bayyana wasu dalilan da yasa za'ayin hakan.
Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce
Gwamnatin tarayya na shirin yi wa yan Boko Haram shari'a a asirce

Bestarewa.com.ng

 ta samu dai cewa jami'in ya ce gwamnatin ta yanke wannan sahawarar ne saboda dalilan tsaro da kuma rahoton da suka samu daga jami'an ta na farin kaya.
Idan mai karatu dai zai iya tunawa, a ranar 9 ga watan gobe ne ake sa ran fara shariar wadanda ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke tsare a wuraren daban-daban kamar yadda muka ruwaito a makon da ya gabata.
Haka ma dai mun samu cewa kimanin yan kungiyar ta Boko Haram din sama da 1,600 ne za'ayi wa shari'ar a wannan lokacin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a

Friday, September 29, 2017

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

September 29, 2017 0 Comments



Gwamnan Jihar Kaduna ya ga abin da ya sa shi kuka a yau
– Malam Nasir El-Rufai ya zubar da hawaye ne dazu a Zaria
– Hakan ya faru ne bayan ya hadu da yaron da aka cirewa idanu

Yau an ga wani bangare na Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai inda ya rusa kuka yayin da ya hadu da wani yaro da matsafa su kayi wa illa a Makarantar Yahaya Hamza da ke Zaria.
El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

Mai Rusau ya rusa kuka dazu a Zaria
Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna yayi kuka har da hawaye yayin da ya je rabawa yara kayan aiki dazu a wata Makaranta a cikin Garin Zaria. Gwamnan ya kai ziyara ne Makarantar da yaron yake wanda aka gyara aka kuma raba wasu na’urorin karatu a Yau Laraba.

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu

El-Rufai ya shara kuka bayan ya hadu da yaron da aka kwakwulewa idanu" width="1200" />
Gwamnan Kaduna El-Rufai yana kuka
El-Rufai yayi kukan ne bayan ya hadu da yaron da wasu matsafa su ka zakulewa idanu kwanakin baya mai suna Sadiq Usman wanda ke da shekaru 5 kacal a Duniya. Gwamnan ya buge da kuka a gaban Jama’a yayin da yaron ya zauna a kan cinyar sa har ta kai yana share hawaye da tsumma.
Kwanaki kun ji cewa mai girma Gwamnan Jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai ya kai ta’aziya ga iyalin Abidu Yazid wanda aka sace surukar sa aka yi garkuwa da ita bayan an kashe mijin ta

Thursday, September 28, 2017

Bashi ya sa Nigeria ficewa daga wasu kungiyoyi

September 28, 2017 0 Comments
Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa kusan 90, sakamakon dawainiyar da ke tattare da mu`amala da kungiyoyin.
Majalisar zartarwar kasar ce ta dauki wannan matakin, tana cewa bashin kudin gudummuwar raya kungiyoyi kadai da ake bin gwamnatin ya zarta dala miliyan 100.
Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, akwai kungiyoyi birjik ko na tsakanin kasa da kasa ko na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma na kungiyar hadin kan Afirka da Najeriya ta shiga cikinsu wadanda kuma dukkansu akwai bukatar gudummuwar da duk kasar da ke cikinsu sai ta bayar a karshen kowacce shekara.
Malam Garba Shehu, ya ce saboda irin wadannan kudaden gudummuwar tafiyar da kungiyoyin wadanda Najeriya ba ta biya ba, har ta kai idan aka je taro akan bukaci mi wkiltar Najeriya da ke wajen ya fita, saboda kawai ana bin kasarsa bashin kudin gudunmmuwar kungiyar.
Ya ce hakan ba karamin abin kunya ba ne ga Najeriya.
Don haka shugaba Muhammadu Buhari ya ce, to ya kamata a sake lale, inda za a baje irin wadannan kungiyoyin a faifai a zabi wadanda ke da amfani ga kasar dan a ci gaba da tafiya tare da su.
Kakakin shugaban Najeriyar, ya kara da cewa wasu basukan da ake bin Najeriyar ma, wani ko shugaban kasa ko kuma minista ne zai je tarukan irin wadannan kungiyoyi ya yi alkawarin cewa, ai Najeriya za ta bayar da gudunmuwar kaza wanda kudin ma babu su a kasa.
Ya ce: ''To irinsu ne suka taru suka yi wa Najeriya yawa, har ta kai ana kunyata ta a wajen taro.''
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a wannan bangare, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu'amala da irin wadannan kungiyoyi.
Malam Garba Shehu, ya ce wadannan basukan ma da aka ce ana bin Najeriyar, tun na shekara da shekaru ne, don haka a kididdige shi ma abu ne mai kamar wuya.
Hak kuma ya yi nuni da cewa, ba matsi ne ya sa Najeriya za ta fice daga wadannan kungiyoyi ba, sanin ciwon kai ne kawai.

Tuesday, September 26, 2017

Shugabanni su tsaya su yi aiki ba zargin Gwamnatocin baya ba - Atiku

September 26, 2017 0 Comments
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa ya koma game da harkar Shugabanci
- Atiku yace Shugabanni su yi aiki ba su yi ta kokawa abin da ya shude ba
- Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta zargi Gwamnatocin baya
Alhaji Atiku Abubakar yayi wasu maganganun da ka iya cewa da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake.
Shugabanni su tsaya su yi aiki ba zargin Gwamnatocin baya ba - Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku tare da Buhari
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Atiku Abubakar ya caccaki irin su Shugaba Muhammadu Buhari a wasu kalamai da yayi a shafin sa na Tuwita jiya kamar yadda mu ka ji. Atiku yayi kira ga Shugabanni da su tsaya su yi aiki ba tare da daura laifin kan wasu ba.
KU KAAtiku yace Shugabanni su tsaya kurum su yi aiki ba wai a tsaya a rika zargin Gwamnatocin baya da yin ba daidai ba. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta yi ta zargin Gwamnatocin baya musamman na Goodluck Jonathan da kashe kasar.
Da alamu dai Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar zai nemi takara a zaben 2019. Kuma a baya Atiku yayi kaca-kaca da Gwamnati mai mulki a wata hira da yayi da Gidan VOA na Amurka.

Monday, September 25, 2017

An kammala shirye-shiryen dawowar Buhari Najeriya daga asibitin Landan

September 25, 2017 0 Comments
a ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar Najeriya gida ranar Litinin bayan kammala abin da ya kai shi London.
Shugaban ya tafi London ne ranar Alhamis bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka.
Daya daga cikin jami'an da suka raka shugaban Amurka ya tabbatarwar da majiyar mu cewa cewa tsarin tafiye-tafiyen mai gidan nasa ya nuna cewa zai koma kasar ne ranar ta Lahadi kamar dai yadda BBC ta ruwaito.
An kammala shirye-shiryen dawowar Buhari Najeriya daga asibitin Landan
An kammala shirye-shiryen dawowar Buhari Najeriya daga asibitin Landan
Bestarewa.com.ng
 dai ta samu cewa kafin tafiyar tasa London, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.Da ma dai fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya.
A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.

Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano

September 25, 2017 0 Comments
Watanni kadan bayan tsohon dan takaran gwamnan jihar Kano Ibrahim Al-amin ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP daga APC, wani tsohon dan majalisar Wakilai Bala Baiko ya tattara nashi-i-nashi ya fice da ga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Ibrahim Baiko ya ce dukkan su ya’yan jam’iyyar ANPP da akayi maja tare aka kafa jam’iyyar APC an yi watsi da su. Ba a komai dasu a jam’iyyar.
Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano
Zaben 2019: Jam'iyyar APC tayi asarar mutane 20,000 zuwa PDP a jihar Kano
ta samu cewa dan siyasar ya ce a lokacin zabe ne kawai aka bukace su amma bayan haka sai akayi watsi da su.
Yace Al-amin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun sha kokawa akan haka kafin Al-amin ya fice daga APC din.Bala Baiko ya ce shi da wasu magoya bayan APC 20,000 ne suka canza sheka zuwa PDP domin su taimakawa jam’iyyar ta sami nasara a zaben 2019 a jihar da kasa baki daya.
“Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kammala shiri tsaf don komawa jam’iyyar PDP.” Inji Bala Baiko.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a

Sunday, September 10, 2017

Video: Akan Dalilin Dayasa Rarara Yayi Wakar – Malam Yaci Kudin Makamai

September 10, 2017 0 Comments
Video : shahararen mawaki wato dauda kahutu rarara kenan  dauke da wasu dalilinasa

Video: Akan Dalilin Dayasa Rarara Yayi Wakar – Malam Yaci Kudin Makamai

To dai nasan kowa yasan waye babban mawakin shiyasa Wanda akeji dashi a nageriya
Babban mawakin shiyasa dauda kahutu rarara Wanda kaf fadin kasar nan yayi fice a wakokin shiyasa
Wanda ya buga wakoki ba adadi na siyasa jam iyyu kala kala.


 

DOWNLOAD VIDEO HERE

Wednesday, September 6, 2017

Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019

September 06, 2017 0 Comments
A cikin wani lamari mai cike da sarkakiya a siyasance, an kama ministar mata da walwalar su ta Gwamnatin Muhammadu Buhari kuma mamba a cikin majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya Hajiya Sanata Jummai Alhasan tana yi wa Atiku Abubakar kamfe din zama shugaban kasa a 2019.
Wannan lamari dai dake da kama da cin amana na dauke ne a cikin wani faifan bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta dauke da hoto da muryar ministar yayin wata ziyarar ban girma da ta kai masa.
Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019
Tirka-Tirka: Ministar Buhari tayi tawaye, ta goyi bayan Atiku matsayin dan takarar ta a 2019
Bestarewa.com.ng
 dai ta samu cewa Sanata Alhasan din kamar yadda ta fada ta jagoranci tawagar shugabannin jam'iyyar APC ne na jihar Taraba tare da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa wajen ta.
Ga dai abunda ta ta fada a cikin bidioyn a takaice: Your excellency Baban mu, shugaban kasar mu inshaAllah a 2019. A gabanka, mutanen kane, magoya bayanka har abada daga jihar Taraba. Sun zo gaisuwar bar girma, gaisuwar Sallah da kuma yi maka murna na wannan daukaka da Allah ya kara maka."
"Yanzu ga su nan, mun zo da Ciyaman din jam'iyya - shine shugaban mu saboda haka gashi nan Alhaji Garba Chedi, ga kuma Coordinator din ka.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a
Bestarewa@gmail.com

Monday, September 4, 2017

LABARI DA DUMI DUMINSA Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Sallah

September 04, 2017 0 Comments
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya watsawa gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje kasa a ido kasa a ido a lokutan shagulgulan bukukuwan Sallah babba da ta gabata kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily Nigerian.
Kamar yadda muka samu daga majiyar tamu, shugaba Buhari ya yi fatali ne da bukatar da gwamnan ya aike masa cewar yana so yazo yayi masa barka da Sallah inda shi kuma Buhari din ya ce baya son duk wani taron siyasa a gidan sa don kuma hutun Sallah yazo.
Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Sallah
Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Salla
Bestarewa.com.ng
 ta samu labarin cewa jami'an tsaron dake gadin shugaban ne dai suka sallami yan aiken Gwamnan daga garin na Daura tun kafin Gwamnan ya taho inda suka fada masu shugaba Buhari yace baya da bukatar ganin Gwamnan.
Haka zalika dai majiyar ta mu ta kuma tabbatar mana da cewa daga nan ne dai kuma sai Gwamnan cikin borin kunya ya canza shawara inda ya ziyarci yayar shugaba Buhari din ya kuma halarci kallon hawan daushe na masarautar garin don kar jama'a su gane akwai matsala.

Sunday, September 3, 2017

[LABARI DA DUMi DUMINSA] An sassari mutane a hawan Daushen Kano

September 03, 2017 0 Comments
Rahotanni daga birnin Kano a Nigeria na cewa an ji wa mutane da dama rauni ciki har da wasu manyan jami'an tsagin siyasar Kwankwasiyya bayan da 'yan daba suka farma mutane a wurin hawan Daushe.
Wasu da suka shaida lamarin sun fada wa BBC cewa wasu 'yan adaban, wadanda ake zargin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, sun farma magoya bayan Tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso, wadanda suka yi fitar dango da jajayen hulanansu.
Suka kara da cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa an yanke su ne da wuka yayin da aka sari wasu da manyan makamai, kamar adda da takofi.
Wani na hannun daman Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa an ji wa manyan jami'ansu da suka hada da tsohon Sakaren Gwamnatin Kano Rabi'u Suleiman Bichi ciwo, kuma ya dora alhakin lamarin kan gwamnatin jihar.
Kawo yanzu rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai game da lamarin. Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba ta hannu ko kadan a lamarin da ya faru.
Sai dai Kwamishinan Yada Labarai na Kano Mohammed Garba ya shaida wa BBC cewa bai san da labarin rikicin ba sai bayan an gama hawan, amma ya ce sun samu bayanan cewa "'yan Kankwasiyya sun shirya tayar da hankali a wurin".
Hawan daushe, wanda sarkin Kano ke jagora kwana daya bayan kowacce sallah, na jan hankalin jama'a da dama ciki har da 'yan yawon bude ido.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu magoya bayan Kwankwasiyya na karbar magani a asibiti da jini a jikinsu.
"Na ga jama'a da dama suna gudu, wasu kuma a kwance, yayin da wasu 'yan Kwankwasiyya suka rinka boye jajayen hulunansu domin kada a gane su," a cewar wani ganau, wanda ya nemi a boye sunansa.
Da dama daga cikin wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibitin koyarwa na Aminu Kano da sauran asibitocin birnin.
Kwamishinan yada labarai Mohammed Garba ya kara da cewa "Mun je wurin, kuma mun dawo lami lafiya, inda jama'a suka yi ta murna suna daga wa Gwamna Ganduje hannu."
Ya kara da cewa dama an saba samun yamutsi a wuirn Hawan Daushe amma dai gwamnati ba ta da hannu a cikin lamarin, kuma ba ta goyon bayan abin da ya faru ko kadan.
Dama dai 'yan siyasa na amfani da hawan na Daushe, wanda ake yi kwana daya bayan sallah, domin nuna karfin magoya bayansu.
Magoya bayan Kwankwasiyya kan yi dandazo da jajayen hulanansu, yayin da su ma magoya bayan Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje ke halatta.

Thursday, August 31, 2017

Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

August 31, 2017 0 Comments
-Jami'iyyar PDP tana son tsaya da Attajiri Aliko Dangote a matsayin dan tarar ta na shugabancin kasa a zaben 2019
-Jami'iyyar ta aike da tawaga domin zawarcin attajirin dan kasuwan
-Jami'iyyar PDP tana sa ran Dangote yayi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jami'iyyar
Bisa ga dukkan alamu, jami'iyyar PDP tana niyyar tsayar da babban attajirin dan kasuwan nan da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.
Rahoton jaridar Daily Times yace PDP tana shirye-shiryen zawarcin attajirin dan kasuwan domin yayi takara a jami'iyyar.
NAIJ.com ta tattaro cewa jami'iyyar zata tsaida dan Arewa ne a matsayin dan takarar shugaban kasa sannan shugabancin jami'iyyar zata koma sashin kudu.
Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Wata majiya a jami'iyyar PDP tace ziyarar da jami'iyyar aka kai ma Alhaji Aliko dangote bazai rasa nasaba ta yi masa tayin tsaya wa takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar.
Majiyar tace tuni an ma riga an aike tawagar da zata je zawarcin Aliko Danote, an yanke shawaran hakan ne bayan kwamitin jami'iyyar wanda ta hada da tsohon shugaba Goodluck Jonathan sun tattauna kuma suka yarda cewa shine ya dace yayi musu takara.

Sunday, August 27, 2017

SHUGABA BUHARI YAYI ALLAH WADARAI DA KALAMAN GWAMNA GANDUJE.

August 27, 2017 0 Comments
Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi tur da Allah wadarai da kalaman gwamna Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Wanda yayi a gidan gwamnatin jihar Kano wajen taron murnar dawowar Buhari gida Nigeria daga kasar Ingila.
Idandai zaku iya tunawa ranar alhamis data gabata ne 24/08/2017 mai taimakawa shugaba Buhari akan kafafen sadarwa Malam Shaaban Ibrahim Sharada ya shirya wani gangami domin nuna farin ciki tare da yin addu’o’i ga shugaba Buhari inda gwamna Ganduje yayi amfani da taron wajen furta kalaman zagi da cin zarafi ga tsohon mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamna Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin Wanda bayason shugaba Buhari ya samu lafiya kuma babban makiyi ga shugaban kasa Muhammad Buhari.
Inda a yammacin yau Shgaba Buhari ya kirawo Sanata Kwankwaso ta wayar tarho yake nisanta kansa da kalaman Gwamna Ganduje.
“Banji dadiba kuma banyi farin ciki da kalaman Ganduje ba, kuma ina mai tabbatar maka babu Wanda zai tsinka kyakkyawar alakar dake tsakanina dakai” cewar Muhammad Buhari.
Daga karshe Shugaba Buhari yayi godiya ga Sanata Kwankwaso da shawarwarin da yake bashi a gwamnatinsa, Sannan yayi hani ga yan siyasa dasu guji Labewa dashi suna cin mutuncin masu mutunci.