Follow Us @soratemplates

Showing posts with label Islamic. Show all posts
Showing posts with label Islamic. Show all posts

Saturday, June 24, 2017

Happy Eid mubarak

June 24, 2017 0 Comments
Happy Eid Mubarak ! Happy Eid Mubarak !! Happy Eid Mubarak !!! The most beautiful phrase on this day which all Muslims utter from their hearts is Eid Mubarak; I also want to have an honor to say it my dear. Eid is coming and we are making our full preparations to spend time with you and sharing this beautiful day. Wish you a sweet day. Across the miles at Eid people who are dear to us are never far away, they’re always close in thought and heart, the way you are today. Wish you and your family the blessings of Allah, kindness of Allah and help of Allah on this day of Eid Mubarak 2  Allah Muslim in the World May Allah Accept Our Ibadah Ameen Suma Ameen ……………From One  Of Ur Lovely Friend…………#ITZ  Suraj Oumar Diso  Happy EID MUBARAK In Advance To Us.

Monday, June 19, 2017

Ramadan Kareem

June 19, 2017 0 Comments
Sheikh Ibrahim Disina


DUNIYA BUDURWAR WAWA!!!
ﺃﻭﻝ ﻣﺎ ﻳﺴﻘﻂ ﻣﻨﻚ ﻋﻨﺪ ﻣﻮﺗﻚ ﻫﻮ ﺍﺳﻤﻚ ..
Farkon abinda da zai bace maka shine
...sunanka
ﻟﺬﻟﻚ ﻋﻨﺪﻣﺎ ﺗﻤﻮﺕ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻨﻚ ﺃﻳﻦ ﺍﻟﺠﺜﺔ .. ؟
Saboda haka ne idan ka mutu zasu ce
gameda kai: Ina gawar?
ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺮﻳﺪﻭﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻴﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺍﺣﻀﺮﻭﺍ
ﺍﻟﺠﻨﺎﺯﺓ .. ؟
A lokacinda za su yi ma sallah su ce, "A
kawo mamacin"
ﻭﻻ ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺈﺳﻤﻚ
Ba za su kiraka da sunanka ba
ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺸﺮﻋﻮﻥ ﺑﺪﻓﻨﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻗﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ
ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺎﺳﻤﻚ !..
Idan za su turbudeka zasu ce "Ku miko da
gawar". Ba za su kiraka da sunankaba
ﻓﻼ ﺗﻐﺮﻙ ﻗﺒﻴﻠﺘﻚ ﻭﻻ ﻳﻐﺮﻙ ﻣﻨﺼﺒﻚ ﻭﻻ ﻧﺴﺒﻚ ..
Kada ka bari kabilarka ko matsayinka ko asalinka ya rudeka ...
ﻓﻤﺎ ﺃﺗﻔﻪ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﺎ ﻧﺤﻦ ﻣﻘﺒﻠﻮﻥ
ﻋﻠﻴﻪ ..
Duniya itace mafi kankantar abu. Inda muka fuskanta ne mafi girman abu.
ﺳﻄﻮﺭ ﻣﻦ ﺫﻫﺐ ..
Ga Wasu Shedaru na Zinari..
ﺍﻟﺤﺰﻥ ﻋﻠﻴﻚ ﺳﻴﻜﻮﻥ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻧﻮﺍﻉ؟؟
Nau'i uku na bakin cikin ne za su kasannce
a gareka??
1- ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻌﺮﻓﻮﻧﻚ
ﺳﻄﺤﻴﺎً ﺳﻴﻘﻮﻟﻮﻥ
ﻣﺴﻜﻴﻦ ‼
1- Mutaneda suka sanka sama-sama za su
ce: Miskini (Bawan Allah)‼
2- ﺃﺻﺪﻗﺎﺅﻙ ﺳﻴﺤﺰﻧﻮﻥ ﺳﺎﻋﺎﺕ ﺃﻭ ﺃﻳﺎﻣﺎً ﺛﻢ
ﻳﻌﻮﺩﻭﻥ ﺇﻟﻰ ﺳﻮﺍﻟﻔﻬﻢ ﻭﺿﺤﻜﻬﻢ ‼
2- Abokanka za su yi bakin ciki na Awowi ko
Kwanaki daga nan sai su koma ga
hidindimunsu da dare-darensu‼
3- ﺍﻟﺤﺰﻥ ﺍﻟﻌﻤﻴﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﺒﻴﺖ ‼ ﺃﻫﻠﻚ ﺃﺳﺒﻮﻉ
ﺃﺳﺒﻮﻋﻴﻦ ﺷﻬﺮ ﺷﻬﺮﻳﻦ ﺃﻭ ﺣﺘﻰ ﺳﻨﺔ ؟؟
3- Tsananin bakin-ciki a cikin gida‼ zai kau
bayan Mako guda ko biyu ko kuma har
tsawon shekara??
ﻭﻣﻦ ﺛﻢ ﺳﻴﻀﻌﻮﻧﻚ ﻓﻲ ﺃﺭﺷﻴﻒ ﺍﻟﺬﻛﺮﻳﺎﺕ ‼
Daga nan kuma za su saka kwandon
‼mantuwa
ﻭﻫﻜﺬﺍﻭﻫﻜﺬﺍ
Haka ne
ﺍﻧﺘﻬﺖ ﻗﺼﺘﻚ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ
Labarinka ya kare a tsakanin mutane.
ﻭﺑﺪﺃﺕ ﻗﺼﺘﻚ ﻣﻊ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﻴﻪ؟؟؟؟؟
Kissarka zata soma a Matabbata??????
ﻭﻫﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ
It a ce Lahira
ﻟﻘﺪ ﺯﺍﻝ ﻋﻨﻚ؟؟؟
Lalle ka rasa???
-1 ﺍﻟﺠﻤﺎﻝ
2- ﻭﺍﻟﻤﺎﻝ
3- ﻭﺍﻟﺼﺤﺔ
4- ﻭﺍﻟﻮﻟﺪ
5- ﻟﻘﺪ ﻓﺎﺭﻗﺖ ﺍﻟﺪﻭﺭ ﻭﺍﻟﻘﺼﻮﺭ
6- ﻭﺍﻟﺰﻭﺟﺔ ؟؟؟
1. Kyawo
2.da Dukiya
3.da Lafiya
4. da 'Ya'ya
5. Lalle ka rabuda Gidaje da Benaye.
6 da Mata???
ﻭﺑﺪﺃﺕ ﺍﻟﺤﻴﺎﺓ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﻴﺔ
ka soma tabbatacciyar rayuwa
ﻭﺍﻟﺴﺆﺍﻝ ﻫﻨﺎ :
ﻭﺍﻟﺴﺆﺍﻝ
Tambaya a nan itace:
ﻣﺎﺫﺍ ﺃﻋﺪﺩﺕ ﻟﻘﺒﺮﻙ ﻭﺁﺧﺮﺗﻚ؟؟؟؟؟؟؟؟؟
mene ne ka tanada domin Kabarinka da
Lahirarka?????????
ﻫﺬﻩ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺗﺤﺘﺎﺝ ﺍﻟﻰ ﺗﺄﻣﻞ ؟؟؟؟؟؟؟؟؟؟
wannan gaskiya ce da ke bukatar
tunani????????
ﺍﺣﺮﺹ ﻋﻠﻰ ؟؟
To ka kiyaye da??
-1 ﺍﻟﻔﺮﺍﺋﺾ
2- ﺍﻟﻨﻮﺍﻓﻞ
3- ﺻﺪﻗﺔ ﺍﻟﺴﺮ
4- ﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺢ
5- ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ
ﻟﻌﻠﻚ ﺗﻨﺠﻮ
1. Farillai
2. Nafilo.
3. Sadaka a boye.
4. Sallar Dare
wata kilan ka tsira
ﻟﻮ ﺳﺎﻋﺪﺕ ﻋﻠﻰ ﺗﺬﻛﻴﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻬﺬﻩ ﺍﻟﻤﻘﺎﻟﺔ ﺇﻥ
ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ
da kuma zaka iya taimkawa wajen
fadakrada mutane akan wannan maganar .
Da yardar Allah:
ﺳﺘﺠﺪ ﺃﺛﺮ ﺗﺬﻛﻴﺮﻙ ﻓﻲ ﻣﻴﺰﺍﻧﻚ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ
Zaka samu tasirin tunatarwarka a
ma'auninka ranar Kiyama.
‏( ﻭﺫﻛّﺮ ﻓﺈﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮﻯ ﺗﻨﻔﻊُ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ )
(ka tunatar lalle tunatarwa na amfanar
Muminai)
ﻟﻤﺎﺫﺍ ﻳﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﻤﻴﺖ
me Ya sa Mamaci ke Sabin
“ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ”
ﻟﻮ ﺭﺟﻊ ﻟﻠﺪﻧﻴﺎ
Sadaka
Da zai dawo a Duniya.
ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ
kamar dai yadda Madaukakin Sarki ya ce:
ﺭﺏ ﻟﻮﻻ ﺃﺧﺮﺗﻨﻲ ﺇﻟﻰ ﺃﺟﻞ ﻗﺮﻳﺐ
‼ ﻓﺄﺻﺪﻕ ‼
Ya Ubangiji da dai ka dan yimini jinkiri
zuwa wani dan lokaci
‼domin in yi Sadaka‼
ﻭﻟﻢ ﻳﻘﻞ :
Kuma bai ce:
domin in yi Umrah
Ko Sallah
Ko Azumi ba.
ﻻﻋﺘﻤﺮ
ﺍﻭ ﻷﺻﻠﻲ
ﺃﻭ ﻷﺻﻮﻡ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ :
ﻣﺎ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺇﻻ ﻟﻌﻈﻴﻢ ﻣﺎ ﺭﺃﻯ ﻣﻦ ﺍﺛﺮﻫﺎ
ﺑﻌﺪ ﻣﻮﺕ ‼
Malamai sun ce:
Mamaci bai ambaci Sadaka ba face sai domin
irin girman tasirinta ne da ya gani a bayan
mutuwa.
ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ
ku yawaita yin Sadaka
ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻲ ﻇﻞ ﺻﺪﻗﺘﻪ
hakika Mumini zai kasance a karkashin
inwar Sadakarsa a ranar Kiyama.
ﻭﺃﻓﻀﻞ ﺻﺪﻗﺔ ﺗﻔﻌﻠﻬﺎ ﺍﻵﻥ ﻫﻲ :
Mafificiyar Sadakar da zaka yi a yanzu itace :
ﻧﺸﺮ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﺑﻨﻴﺔ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ
Yada Wannan magana da niyyar yin Sadaka
ﻷﻥ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺳﻴﻄﺒﻖ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻭﻳﻌﻠﻤﻪ ﻟﻸﺟﻴﺎﻝ
ﺍﻟﻘﺎﺩﻣﺔ ﻓﺄﺟﺮﻩ
Dominduk wanda ya Aiwatar da Wannan
magana, to Ladarsa
ﻳﺼﻠﻚ ﺑﺈﺫﻥ ﺍﻟﻠﻪ
Zata sadu da kai da izinin Allah

Ramadan Kareem

June 19, 2017 0 Comments
*LAYLATUL QADR*

*🔜 Aisha (R.A) ta ruwaito cewa: Annabi (S.A.W) yace: "Kunemi daren laylatul qadr a goma qarshe na watan ramadan*
               *(Bukhari)*


*🔜 Aisha (R.A) Ta tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa: "Idan na riski daren laylatul qadr wane addu'a zanke karantawa?*

*🔜 Sai Manzon Allah yace mata:*    *(ALLAHUMMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFUWA FA'AFU ANNA)*  *Ya Allah lalle kaine  mai yin afuwa, Ina neman afuwanka, Kayi mana afuwa*
            *(Tirmizi)*


*🔜 Anas (R.A) ya ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W) yace: "Lokacin da laylatul qadr zai kasance Mala'ika Jibrilu (A.S) zai sauqo da tawaga masu yawa na Mala'iku zuwa duniya suna neman rahama ga masuyin sallah.*

*Kuna ambaton Allah da wasu ayyuka na ibadah*
          *(Shu'abul imaan)*


*🔜 Allah Ta'alah yana sauqowa daga sama zuwa qasa tare da wasu runduna na Mala'iku da kuma Mala'ika Jibrilu suna nema mana (Rahama, Gafara, Afuwa, Aminci) bazasu gushe ba har sai zuwa fitowar alfijir*
         *(Suratul Qard)*


*Ana dacewa da wannan ranan acikin darare kamar haka*

*21st*  *23rd*   *25th*   *27th*  *29th*

*Allah ya datar damu da wannan dare mai albarka*

Friday, June 2, 2017

RAMADAN KAREEM

June 02, 2017 0 Comments
*YAYA MATSAYIN AZUMIN WANDA BAYA SALLAH, SHIN YANADA AZUMI?*

الحمدلله.

Amsa:Wanda baya sallah ba'a karbar aikinsa na azumi ko zakkah ko hajji, ko duk wani aiki.

Imamul bukhari yaruwaito hadisi (520) daka buraida yace: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:( Duk wanda yabar sallar la'asar hakika ya rusa aikinsa).

Ma'anar yabata aikinsa shine yarushe bazai amfaneshi ba, wannan hadisi yanuna wanda baya sallah ba'a karbar aikinsa, wanda baya sallah bazai amfana dakomai na aikin saba, aikinsa baza'a kaishi zuwa ga Allah ba.

Ibnul qayyeem rahimahullah yace: dangane da ma'anar wannan hadisin acikin littafinsa Assalah (65)

" Abunda yabayyana acikin hadisin, barin sallar iri biyune,barin sallah na har abada shi kwata kwata bayayi wannan yana bata aikinsa gaba daya, da kuma barinta na wani lokaci kamar wuni guda sananne wannan yana bata aikinsa na aiya wannan yinin, Barin sallah gaba daya shike lalata aikinsa gaba daya, barinta na wata rana yana bata aikin wannan ranar ko ranakun dabaya sallar.


An tambayi shaik usaimin acikin fatawarsa (87) game da hukuncin azumin wanda baya sallah.

Saiya amsa; Wanda baya sallah azuminsa ba ingantacce bane ba karbabbe bane, domin wanda baya sallah kafirine wanda yayi ridda saboda fadin Allah madaukakin sarki:

فإن تابوا وأقموا الصلاة وآتوا الزكوة فإخوانكم في الدين.  التوبة/ 11

Idan sun tuba sun tsaida sallah sunbada zakkah to sunzama 'yan'uwanku a'addini.

Dafadin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( Banbanci  dake tsakanin musulmi dawanda bashiba shine yin sallah wanda yabar sallah hakika yakafirta) Turmuzi ( 2621) Albani ya ingantashi acikin sahihu turmuzi.

Saboda kuma shine maganar sahabbai gaba dayan imma baizama ijma'insu akaiba, Abdullahi bin shaqeeq rahimahullah yana cikin tabi'ai wadanda suka shahara yace: Sahabbai sunkace basa ganin wani aiki cikin ayyuka wanda barinsa kafircine inba sallah ba, abisa wannan idan mutum yai azumi kuma baya sallah to azuminsa anmayar masa baza'a karba masaba, kuma bazai amfaneshiba ranar alkiyama, zamuce dashi yi sallah sannan kai azumi, amma kai azumi baka sallah azuminka ba karbabbe bane za'a mayar maka saboda kafiri ba'a karbar duk wata ibada tasa.

An tambayi malaman lajnatul da'imah ( 10/140) tambaya kamar haka:idan mutum yakanyi kwadayin yin azumi kuma yana sallah da azumi amma kuma dazarar azumi yawuce shikenan yadena sallah, shin yana da azumi?

Sai suka amsa: sallah rukunice daga cikin rukunan musulunci muhimmai wanda daka kalmar shahada sai ita, tana cikin farillai na tilas wajibi, duk wanda yabar sallah yana maikore wajabcinta ko kuma saboda wulakantata ko saboda kasala hakika yakafirta, amma masu azumi suna sallah acikin azumi kawai wadannan suna yaudarar Allah ne,tir da mutanen dabasu san Allah ba sai awatan azumin ramazhaan, azuminsu bai ingantaba tare dabarin sallarsu alokacinda ba na azumi ba, sudin kafiraine kafirci babba, koda basu kore wajabcin sallar ba amafi inganci maganganun malamai.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

🌙Tambayoyin Musulunci🌙

+


🌙MARHABA🌹 RAMADAN🌙

Wednesday, May 31, 2017

May 31, 2017 0 Comments
FALALAR YIN SALLAR ASHAM

Ankarbo daga sayyadi Aliyu dan Abi Dalib (RTA) yace
Na tambayi manzon Allah (SAW) acikin Falalar yin sallar Asham Acikin wata Ramadan sai Manzon Allah (SAW) yace
Wanda yayi Asham adare na farko Awatan Ramadan mumini yana fita daga cikin laifinsa kamar yadda mahaifiyarsa ta haifeshi,
Wanda yayi Asham Adarena 2 Allah zai gafartawa iyayansa,
Wanda yayi Asham Adare na 3 Wani Mala'ika zaikira sunansa a karkashin Al'arshi yace Anunka aiyukan Alkhairi kuma agafarta laifukansa,
Wanda yayi Asham Adare na 4 za'a bashi ladan wanda yakaranta Attaura, Injila, zabura, da Alqur'ani,
Wanda yayi Asham Adare na 5 Za'a ladan yayi sallah a makka da Madina,
Wanda yayi Asham Adare na 6 za'a bashi ladan mala'ikun da suke kewaye da Baitul ma'amuri kuma dukkan dutse da marmara zasu nemi agafarta masa laifukansa,
Wanda yayi Asham Adare na 7 kamar yariski Annabi musa ne yataimakeshi akashe Fir'auna da Hamana,
Wanda yayi adare na 8 Allah zaibashi ladan daya bawa Annabi Ibrahim,
Wanda yayi adare na 9 Kamar ya bautawa Allah ne irin wadda Annabi Muhd (SAW)
Yayiwa Allah,
Wanda yayi adare na 10 Allah zai'azurtashi Da Alkhairan duniya da lahira,
Wanda yayi adare na 11 zai fita daga duniya kamar yadda aka haifeshi,
Wanda yayi adare na 12 zaizo ranar Alkiya yana Amintacce
Wanda yayi adare na 13 Allah zaigina masa birni Agidan Aljanna,
Wanda yayi adare na 14 Mala'iku zasuzo suyi masa shaidar yayi sallar Asham baza aimasa hisabiba,
Wanda yayi adare na 15 Mala'iku zasuyi masa salati da madauka Al'arshi da kursiyu,
Wanda yayi adare na 16 Allah zai rubuta sunansa daga masu kubuta daga wuta,
Wanda yayi adare na 17 za'a bashi lada kamarna dukkan Annabawa,
Wanda yayi adare na 18 wani mala'ika zai kiransa yace yakai bawan Allah
Allah ya yarda dakai da mahaifanka,
Wanda yayi adare na 19 Allah zaidaga matsayinsa a Aljanna Firdausi,
Wanda yayi adare na 20 Allah zaibashi ladan shahidai da salihan bayi
Wanda yayi adare na 21 Allah zaigina masa daki a Aljanna da haske,
Wanda yayi adare na 22 zaizo ranar Alkiyama yana Amintacce daga bakin ciki
Wanda yayi adare na 23 Allah zaigina masa gida a Aljanna,
Wanda yayi adare na 24 za'a amsa Addu'o insa guda 24,
Wanda yayi adare na 25 za'a dauke masa azabar kabari,
Wanda yayi adare na 26 za'a taramasa ladan shekara Arba'in,
Wanda yayi adare na 27 zaifice ranar Alkiyama Akan siradi kamar walkiya,
Wanda yayi adare na
28 za'a daga martabarsa sau dubu,
Wanda yayi adare na  29 Allah zaibashi ladan Aikin hajji dubu karbabbu,
Wanda yayi adare na 30 Allah zaice..............


WASSALAM


​BY ABBA YAHAYA ABDULLAHI

ADDU.A YAYIN KIRAN SALLAH.

May 31, 2017 0 Comments
Addu’a yayin kiran Sallah :
Wanda ya ji kiran sallah zai fadi dukkan abin da ladanin yake fadi, sai dai idan yace;
ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﺼَّﻼَﺓِ، ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻔَﻼَﺡِ .
Hayya Alas Salah, Hayya Alal Falah.
Ku taho ga Sallah, ku taho ga babban rabo.
Maimakon haka sai shi ya ce:
ﻻ ﺣَـﻮْﻝَ ﻭَﻻ ﻗُـﻮَّﺓَ ﺇِﻻّ ﺑِﺎﻟﻠﻪ .
La hawla wala kuwwata illa billah.
Babu daraba, babu karfi sai da Allah.
ﻭَﺃَﻧﺎ ﺃَﺷْـﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَـﻪَ ﺇِﻻّ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْـﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَـﺮﻳﻚَ ﻟَـﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣﺤَﻤّـﺪﺍً ﻋَﺒْـﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُـﻮﻟُﻪُ ، ﺭَﺿِﻴـﺖُ ﺑِﺎﻟﻠﻪِ ﺭَﺑَّﺎً ، ﻭَﺑِﻤُﺤَﻤَّـﺪٍ ﺭَﺳُـﻮﻻً ﻭَﺑِﺎﻹِﺳْﻼﻡِ ﺩِﻳﻨًﺎ .
Wa-ana ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-anna Muhammadan AAabduhu warasooluh, radeetu billahi rabban wabimuhammadin rasoolan wabil-islami deena.
Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini.
Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sannan ya ce:
ﺍﻟﻠّﻬُـﻢَّ ﺭَﺏَّ ﻫَﺬِﻩِ ﺍﻟﺪّﻋْـﻮَﺓِ ﺍﻟﺘّـﺎﻣَّﺔِ ﻭَﺍﻟﺼّﻼﺓِ ﺍﻟﻘَـﺎﺋِﻤَﺔ ﺁﺕِ ﻣﺤَـﻤَّﺪﺍً ﺍﻟﻮَﺳﻴـﻠﺔَ ﻭَﺍﻟْﻔَﻀـﻴﻠَﺔ ﻭَﺍﺑْﻌَـﺜْﻪُ ﻣَﻘـﺎﻣًـﺎ ﻣَﺤْـﻤُﻮﺩﺍً ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻭَﻋَـﺪْﺗَﻪُ ﺇِﻧَّـﻚَ ﻻ ﺗُـﺨْﻠِﻒُ ﺍﻟْﻤِﻴـﻌَﺎﺩَ .
Allahumma rabba hathihid-da'watit-tammah, wassalatil-ka-imah ati Muhammadan alwaseelata wal-fadeelah, waba'ath-hu makaman mahmoodan allazee wa'adtahu, innaka la tukhliful-mee'ad.
Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.
Sannan ya yiwa kansa addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu'a a wannan lokaci ba a kin karbarta

Saturday, May 27, 2017

RAMADAN KAREEM

May 27, 2017 0 Comments
WASU NASSOSHI DAGA QUR'ANI DA SUNNAH AKAN FALALAR AZUMI:

1- قال الله تعالى: (شهر رمضان الذي أنزل فيه القرآن) الآية[سورة البقرة].

Allaah madaukakin Sarki Yana cewa: (Watan Ramãdan wanda a cikin Sa aka saukar da Al -QUR'ÃNI).

2-  عن أبي أمامة رضي الله عنه أنه قال: يا رسول الله، مرني بأمر ينفعني الله به، قال: (عليك بالصوم فإنه لا مثل له) رواه النسائي وهو حديث ثابت.

Daga Abu-Umãmatal Bãhiliy (r.a) yace: Ya Manzon Allaah ka umurceni da wani al'amari wanda Allaah zai amfaneni wurin Allaah, Sai Manzon Allaah(saw) Yace: (Ka lizimci azumi, saboda babu irinshi).
3- عن سهل بن سعد رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وآله وسلم قال: (إن في الجنة بابا يقال له الريَّان، يدخل منه الصائمون يوم القيامة، لا يدخل منه أحد غيرهم، يقال: أين الصائمون؟ فيقومون، لا يدخل منه أحد غيرهم، فإذا دخلوا أغلق، فلم يدخل منه أحد) متفق عليه.

Daga Sahl bn Sa'ad (r.a) Lallai Annabi (saw) Yace: (A Aljannah akwai kofa da ake kiran shi AR-RAYYÃN, masu azumi zasu shiga ta cikin shi ranar Al- Qiyãmah, babu wanda zai shiga ta kofar sai su. Za'a ce ina masu azumi? Sai su mi'ke, babu wadanda zasu shiga ta wannan kofar sai su, idan suka shiga sai a kulle, saboda haka babu wanda zai sake shiga bayan su).

4-  قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (يا معشر الشباب! من استطاع منكم الباءة فليتزوج، فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج، ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء) متفق عليه.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Yaku matasa! Wanda yake da hali yayi aure, saboda shi yafi kame ido (gani) dakuma kiyaye farji, wanda kuma bashida halin aure to yayi azumi; domin azumi kamar dandaqa ne (yana rage sha'awa).

5- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (الصوم جُنَّة يَستجن بها العبد من النار) رواه أحمد وهو ثابت أيضا.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi garkuwa ne da bawa ke kare kanshi daga shiga wuta).

6- عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (قال الله تعالى: كل عمل ابن آدم له إلا الصيام، فإنه لي وأنا أجزي به )، وفي رواية لمسلم: (كل عمل ابن آدم يضاعف، الحسنة بعشر أمثالها إلى سبعمائة ضعف، قال الله عز وجل: إلا الصوم، فإنه لي وأنا أجزي به، يدع شهوته وطعامه من أجلي) متفق عليه.

Daga Abū Harairah (r.a) yace: Manzon Allaah (saw) Yace: (Allaah SWT Yace: Kowane aiki na dan adam ne banda azumi, domin azumi nawa ne kuma NI zan bada sakamakon shi), A riwayar Muslim kuwa Yace: (Ana ninka kowane aiki na dan adam,  kowane lada za'a ninka shi sau goma har zuwa ninki ďari bakwai, sai Allaah Yace: sai azumi, domin shi nawa ne kuma NI ne zanyi sakayya akansa, dan adam yakan bar sha'awar shi da  abincin shi da saboda NI).

7-  قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (الصيام والقرآن يشفعان للعبد يوم القيامة، يقول الصيام: أي رب منعته الطعام والشهوات بالنهار فشفعني فيه، ويقول القرآن: منعته النوم بالليل فشفعني فيه، قال: فيُشَفَّعان). رواه أحمد وهو حديث ثابت.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi da Al - Qura'ni zasu ceci bawa ranar Al-Qiyãmah, azumi zaice: Ya Ubangiji na hanashi abinci da abubuwan sha'awa da rana Kabani ceton shi, shi kuma Qur'ani zaice: Na hanashi bacci da dare dan haka kabani ceton shi, sai Manzon Allaah Yace: Sai abasu ceton su).

8- قال رسول الله صلى عليه وآله وسلم: (من صام يومًا في سبيل الله باعد الله وجهه عن النار سبعين خريفا) متفق عليه.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Duk wanda ya azumci rana ďaya dan Allaah, Allaah Zai nisantar da fuskar shi daga wuta tsawon shekaru saba'in).

9-  قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (للصائم فرحتان: فرحة عند فطره، وفرحة عند لقاء ربه، ولخلوف فم الصائم أطيب عند للله من ريح المسك) متفق عليه.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Mai azumi yanada farin ciki biyu: Farin ciki sanda zaiyi buďa baki, da Farin ciki lokacin haďuwa da Ubangijin shi, Tabbas! Bashi (wari) na bakin mai azumi yafi 'kanshin almiski kyawu da daďi a wurin Allaah).

10-  قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (فتنة الرجل في أهله، وماله، وجاره تٌكِّفرها: الصلاة، والصيام والصدقة) رواه البخاري.

Manzon Allaah (saw) Yace: (Fitinar mutum a iyalinshi, da dukiyarshi, da ma'kwabcinshi; Sallaah da Azumi da Sadaqah suna kankare su).

11- عن زيد بن خالد الجهني رضي الله عنه  قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم -: (من فطر صائمًا كان له مثل أجره غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيئًا) رواه الترمذي وابن ماجه وهو ثابت.

Daga Zayd bn Khalid Al-Juhaniy (r.a) Yace: (Duk wanda yacida mai azumi Allaah zaibashi kwatankwacin ladan shi batareda an rage ko kadan daga ladan mai azumin ba).

12- عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وآله وسلم قال: (ثلاثة لا تردُّ دعوتهم: الإمام العادل، والصائم حتى يفطر، ودعوة المظلوم) رواه الترمذي وابن ماجه وهو حديث ثابت أيضا.

Daga Abu Hurairah (r.a) Annabi (saw) Yace: (Mutane uku ba'a mayar da addu'ar su: Jagora adili, Mai azumi har zuwa buďa bakin sa, dakuma addu'ar wanda aka zalunta).

Allaah Ya amshi ibadojin mu.

Ďan'uwanku:   A Y A

RAMADAN KAREEM

May 27, 2017 0 Comments
Addu'a Idan Mai Azumi Zai Buda Baki
ذَهَبَ الظَّمَأُ، وَابْتَلَّتِ العُرُوقِ، وَثَبَتَ اْلأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ.
Zahabaz-zama-o wabtallatil-'urooq, wathabatal- ajru in shaal-lah.

Kishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah Ya so.

Abdullahi bn Amr bn Al-As ya ce Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Mai azumi yana da addu'a da ba a mayar da ita idan ya zo bude baki". Abdullahi bn Amr ya kasance idan ya zo buda baki sai ya ce;
اللّهُمَّ  إِنَّي أَسْأَلُكَ بِرَحْمَتِكَ الّتي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ، أَنْ تَغْفِرَ لِي .
Allahumma inne as-aluka birahmatikal-latee wasi'at kulla shay'i, an taghfira lee.

Ya Allah! Ina rokon Ka saboda Rahamarka da ta yalwaci komai, Ka gafarta mini.

Tuesday, May 9, 2017

RAMADAN KAREM

May 09, 2017 0 Comments
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته

It is possible that one day I have spoken in your absence about you, the language, whether I am alone or with an assembly, deviates incontestably, voluntarily or involuntarily. I hope that you will forgive me if I have been slandering you. I KNOW THAT ALLAH WILL NOT FORGIVE ME AS MY PERSON ON WHICH I SPEAKED IN HIS ABSENCE DOES NOT DISPUTE ME FIRST. I send this message to all my contacts, not out of weakness on my part but out of fear of the one who holds all the kingdoms.

If you have forgiven me send me this message which is an invitation to mutual forgiveness.
Purify our souls, forgive me, for sudden deaths are frequent.
I take *Allah as A Witness* that I forgive you.

Let this message be a mutual invitation to forgiveness & purification  before Ramadan! 🙏🙏🙏