Follow Us @soratemplates

Showing posts with label Kannywood. Show all posts
Showing posts with label Kannywood. Show all posts

Wednesday, April 25, 2018

Kannywood : Babu Yadda Za’a Yi In Daina Sana’ar Fim – Sapna Aliyu

April 25, 2018 0 Comments
na yin wasu harkoki na kasuwanci ko na sana’a ba, sai dai kawai mace ta ce ita ’yar fim ce. To, amma a yanzu yanayi ya canja, ta yadda za ka ga da damansu a yanzu kowacce ta na yin harkokin kasuwancinta.
SAPNA ALIYU MARU na daya daga cikin jaruman fim mata da a yanzu su ke sahun manyan ’yan kasuwa, da ta ke shige da fice a cikin kasashe domin saye da sayarwa. Baya da kantin da ta bude a Dantsoho Plaza da ke titin Abdullahi Bayero a Kano.
WAKILIN LEADERSHIP A YAU ya tattauna da jarumar a game da yadda take gudana da kasuwancinta a matsayinta na jarumar finafinan Hausa. Shin ta daina aikin ne ko kuma tudu biyu take ci? Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasnace.
Sapna, sunanki ba boyayye ba ne a masana’antar finafinai ta Kannywood, amma dai za a iya cewa sama da shekara daya kenan an rabu da ganin ki. Wannan ya sa a ke ganin kamar kin bar harkar fim ne.
“Eh, haka ne, amma dai ni abin da zan fada Sapna dai ba ta daina yin fim ba, don fim sana’ata ce, babu yadda za a yi na daina, sai dai idan na yi aure kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi. Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shafi harkar kasuwanci wanda a yanzu su na saka a gaba. Kuma a yanzu ma fim na daina fitowa a ciki ban daina furodusin ba, kawai dai ba na fitowa ne a ciki.”
Kamar wanne irin kasuwanci ki ke yi?
“To, kasuwanci na yanzu ka ga a kantina ka zo ka same ina sayar da kayayyaki irin su atamfofi, leshi, takalma, agogo da ‘yan kunnaye da jakunkuna. To kuma wannan harkar ta sa ina da karancin lokacin da zan rinka zuwa lokeshin, saboda shi fim yana bukatar cikakken lokaci to ni kuma a yanzu ba ni da shi. Don haka idan na karbi aikin mutane ban san yadda zan yi a shi ba. Saboda kula da kanti da kuma zuwa na kawo kaya. Amma dai nan gaba kadan idan na gama saita harkokina masoyana za su ci gaba da ganina a fim.”
A yanzu kin kai tsawon wanne lokaci ba ki fito a fim ba?
“To, ina ganin dai a yanzu na fi shekara don tun fim dina mai suna Watarana, da muka yi fim din da Adamu a Kaduna, ina ganin tun daga ban kara fitowa ba.”
A matsayinki na jaruma, furoodusa, ko ya ya kike kallon harkar fim a wannan lokacin?
“To, gaskiya ana samun cigaba sosai don na ga ana fita aikin fim a koda yaushe don haka ci gaba ake samu da ko a baya aka samu ba za a samu haka ba, don haka an samu ci gaba ta kasuwa da kuma kayan aiki, ni dai a yadda nake gani kenan.”
Me ya sa a yanzu ba a samun jarumai masu yawa da ake yayi, kamar da sai ki ga mata da yawa ana yayinsu amma a yanzu sai dai daya ko biyu?
“To, abin da ya sa yanzu idan ka duba a ba cika tsayawa ba a fim kadai kusan kowacce jaruma tana da harkokinta na kasuwanci da take yi don haka yanzu an daina tsayawa ana jiran a yi fim sai ake hadawa da kasuwanci. To irin wannan sai ka ga wata ma idan ana neman ta ta fito a fim sai ka ga ba ta a lokaci kamar a baya don haka za ka ga duk an ragu wasu kuma sun yi aure ba a samu wadanda suka maye gurbin su ba. ”
Amma ba kya ganin a matsayinki na ‘yar kasuwa nan gaba idan kika dawo za ki yi fim sai a ga kudin da za a ba ki sai furodusa ya shirya don kada ki raina?
“Ai ba haka ba ne shi dan fim duk wata alfarma da ya samu a duniya ta hanyar fim ce, don haka duk ina ya je ya dawo fim ne gatansa, don haka ko nawa za a bai wa mutum ba zai raina ba. Don tun kadin ya zama wani abu ya san haka ake biyan a don haka ba wani abu ne daban ba.”
To, ya ya kike iya gudanar da kasuwancinki a matsayinki na jaruma da kowa ya san fuskarki?
“Ina jin dadi sosai don ka ga su ‘yan fim suna da alfarma. Sau da yawa idan na je waje ko da ana hana mutane shiga sai ka ga an bar ni na shiga. Aga an ga ni ‘yar fim ce. Don haka ina jin dadin sosai kuma wasu ma saboda sun san kai dan fim ne suna zuwa sayan kaya wajena. Don su zo su ganni kuma duk fim ne ya ja min wannan alfarma.”
To ya ya mu;malar ki take a yanzu da ‘yan fim?
“Mu’amala ta tana nan kamar dai muna tare da su kamar tare muke kuma na fada maka ina furodusin don haka koyaushe muna tare sai dai idan na tafi wajen kasuwancina.”
Daga karshe wace shawara kike da ita musamman ga mata ‘yan fim?
“To, shawarata a garesu ita ce, lokaci ya yi da za su gane harkar fim kadai ba za ta rike su ba. Domin kuwa suna cikin fim din za su yi aure. Kuma idan sun yi aure ba za su ci gaba da fim ba, don haka su raba kafa su rinka hadawa da kasuwanci ta yadda ko da sun yi aure za su ci gaba da yin kasuwancinsu.”
To, madalla mun gode.
“Ni ma na gode.”
-LEADERSHIP

Kannywood: Tsohon Miji Na Auri Saki Ne – Inji Ruqayya Dawayya

April 25, 2018 0 Comments
Tsohuwar fitacciyar jarumar shirin fina finan Kannywood, Rukayya Dawayya ta bayyana matsalolin data fuskanta a rayuwar aure da suka yi sanadin mutuwar auren nata da tsohon mijinta.
Dawayya ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da jaridar Blue Print, inda tace tayi danasanin auren tsohon mijinta Adamu Teku, saboda bata yi cikakken bincike ba game da shi. Auren Dawayya ya mutu ne kimanin shekaru hudu bayan auren, a lokacin da ta kai ma mahaifiyarta ziyara bayan dawowarta Najeriya daga kasar Saudiyya, duk kuwa da sadaukarwar da ta dinga yi don ganin auren ya zauna lafiya.
“Allah na gani na yi iya bakin kokarina don ganin aurena ya zauna lafiya, amma hakan bai yiwu ba, saboda mijina auri saki ne, kafin ni ma ya saki mata sama da 15, don haka ba kai na farau ba. Yarona Arafat ne na 11 a cikin yayansa.
“Banda matan da ya saka kafin su haihu a gidansa, Uwargidarsa ta bayyana min cewar kafin ita ma ya auri mata guda 6, itace ta 7 a yanzu. Kuma gaskiya ban yi bincike game da shi ba a sosao kafin aurenmu, iyakar binciken da nayi shine a Abuja, amm banke kauyensu ba a jihar Adamawa.
“Don har babbar yarsa sai da bayyana min dukkanin halayyarsa, har ma a kauyensu ana cin mutuncin yayansa da sunan wai mahaifinsu baya iya rike matan aure, wanda hakan ya sanya yayan nasa basa iya cudanya da jama’an kauyen.” Inji ta.
Bugu da kari da aka tambayeta game tsawon lokacin da suka yi suna soyayya kafin aure, sai Dawayya tace gaskiya watanni biyu suka yi kacal suna soyayya, sakamakon a wannan lokacin aure kawai take son yi ruwa a jallo, don haka ta rungumeshi ba tare da bata lokaci ba, har suka yi aure.
Daga karshe Dawayya tace tun bayan da ta samu juna biyu ne Adamu ya fara nuna mata fushinsa, saboda wai shi baya son haihuwa, don haka ya gindaya mata munanan sharudda, amma ta cije, har sai ranar da ta kai ma mahaifiyarta ziyara, inda ya aiko mata da sakon saki ta wayar hannu

Sunday, April 15, 2018

Kannywood : Why I’m still single –Fati Bararoji

April 15, 2018 0 Comments

Why I’m still single –Fati Bararoji

blueprint.ng
Apr 14, 2018 11:48 AM
Fati Baffa Bararoji is one of the pioneer actresses in Kannywood. Aside featuring in hit movies, Bararoji had produced two movies: Bakar Tukunya and Jan Ido, before going underground. In this interview with ALIYU ASKIRA in Kano, Bararoji opens up on her relationship, film industry as well as why she is still single.
You used to be a household name in Kannywood, why did you go underground?
Well, I have many reasons why I decided to be very scarce. One, I travel a lot these days, especially to Saudi Arabia, Dubai and India for a jewellery business.
After producing Bakar Tukunya and Jan Ido, I discovered that the industry was no longer what it used to be before. That is why I decided to excuse myself.
So, what is really happening with you?
Well, let me first of all use this medium to call on my fans to pray for me because I am actually desperate to get married and bear children.
I am above 30 years and as a Muslim lady, even my parents are worried that I am still single. But the truth is, good looking guys and even rich men have been toasting me severally. But the issue is, anytime they invite me out, they will request that I follow them to their guest houses or hotels which I don’t like because, if you see a man and a woman, the next person in-between them is Satan. I always avoid that.
This is the why even in my restaurant, if you go there, you hardly see me because I am aware some people go there to have opportunity to invite me out. I don’t know why people are thinking that ladies are either cheap, that with small amount we can zip down for any idiot.
Three years ago, there were rumours that you were set to marry an artist. Why did it not work?
It is a long story, very touching and frustrating. But since you took the pain to come here, I will tell you what happened. The rumour you are talking about was about my proposed marriage to Katsina based singer, Abdu Boda.
This guy had virtually become like a member of our family. He would come to our house and my sisters would even cook for him even if I am not around. Everybody was convinced that he would marry me but all of a sudden, a female friend called me and told me that she saw an invitation sent out by Audu Boda and that the name of the proposed bride is not Fati Baffa.
On hearing such sad news, I almost fainted. Then I decided to call him. Do you know what?
The day I called him was the day his wedding was to take place but do you know that this guy swore to me that what I heard was not true, and actually, it turned out that Audu Boda wedded another lady on the day in question.
Trust me, I dressed up quickly, took a drop to Katsina and attended the reception. I pretended that I was not hurt. However, despite all these, I still love him up till tomorrow. I have nothing against him.
So, how did you overcome the heartbreak?
I quickly went to Umrah and prayed hard to my creator to give me the strength to overcome this shock of the century. Since then, I have continued with my life, praying day and night for God to give me my own man.
You see, as a lady who all her mates are married, I always feel odd and rejected. Whenever I attend events in Kannywood, I see faces of new-breeds. I mean, they are set of actresses that one is old enough to have them as children. As a result, I always feel like retiring completely from the Industry.
However, I still relate with them so much, especially the old friends like Sadiya Gyale, Rukaiyya Dawaiya, Saima Muhammad, Rashida Adamu, and Asmau Sani. I feel comforted whenever I am in their midst.
Finally, your contemporaries in the industry appear to be doing you in terms of material acquisition. What is really happening?
Well, I don’t know how to answer this question. Let me try this: Somebody once told me when a pregnant female student was being interrogated by her principal of the person responsible for the pregnancy, she burst into tears and swore by the Holy Quran that she is a virgin.
I also read a conversation between a prostitute and a politician. The politician told the prostitute to trust him because he is a decent person. Then the lady in question told the politician that he should trust her or even marry her if possible because after being a prostitute for years, she is still a virgin. I believe you understand what I mean?
If I want to mess up, I would have been a proud owner of chains of cars now. Instead, you can see me selling food and taking the risk of travelling to Saudi Arabia, Dubai and India to earn decent living. So, if bottled water is as pure as people claim, then Fati Baffa is as pure as bottled water.
I am above 30 years and as a Muslim lady, even my parents are worried that I am still single. But the truth is, good looking guys and even rich men have been toasting me severally. But the issue is, anytime they invite me out, they will request that I follow them to their guest houses or hotels which I don’t like because, if you see a man and a woman, the next person in-between them is Satan. I always avoid that.
This is the why even in my restaurant, if you go there, you hardly see me because I am aware some people go there to have opportunity to invite me out. I don’t know why people are thinking that ladies are either cheap, that with small amount we can zip down for any idiot.
Three years ago, there were rumours that you were set to marry an artist. Why did it not work?
It is a long story, very touching and frustrating. But since you took the pain to come here, I will tell you what happened. The rumour you are talking about was about my proposed marriage to Katsina based singer, Abdu Boda.
This guy had virtually become like a member of our family. He would come to our house and my sisters would even cook for him even if I am not around. Everybody was convinced that he would marry me but all of a sudden, a female friend called me and told me that she saw an invitation sent out by Audu Boda and that the name of the proposed bride is not Fati Baffa.
On hearing such sad news, I almost fainted. Then I decided to call him. Do you know what?
The day I called him was the day his wedding was to take place but do you know that this guy swore to me that what I heard was not true, and actually, it turned out that Audu Boda wedded another lady on the day in question.
Trust me, I dressed up quickly, took a drop to Katsina and attended the reception. I pretended that I was not hurt. However, despite all these, I still love him up till tomorrow. I have nothing against him.
So, how did you overcome the heartbreak?
I quickly went to Umrah and prayed hard to my creator to give me the strength to overcome this shock of the century. Since then, I have continued with my life, praying day and night for God to give me my own man.
You see, as a lady who all her mates are married, I always feel odd and rejected. Whenever I attend events in Kannywood, I see faces of new-breeds. I mean, they are set of actresses that one is old enough to have them as children. As a result, I always feel like retiring completely from the Industry.
However, I still relate with them so much, especially the old friends like Sadiya Gyale, Rukaiyya Dawaiya, Saima Muhammad, Rashida Adamu, and Asmau Sani. I feel comforted whenever I am in their midst.
Finally, your contemporaries in the industry appear to be doing you in terms of material acquisition. What is really happening?
Well, I don’t know how to answer this question. Let me try this: Somebody once told me when a pregnant female student was being interrogated by her principal of the person responsible for the pregnancy, she burst into tears and swore by the Holy Quran that she is a virgin.
I also read a conversation between a prostitute and a politician. The politician told the prostitute to trust him because he is a decent person. Then the lady in question told the politician that he should trust her or even marry her if possible because after being a prostitute for years, she is still a virgin. I believe you understand what I mean?
If I want to mess up, I would have been a proud owner of chains of cars now. Instead, you can see me selling food and taking the risk of travelling to Saudi Arabia, Dubai and India to earn decent living. So, if bottled water is as pure as people claim, then Fati Baffa is as pure as bottled water. copyright protection, only an abstr

Saturday, March 24, 2018

Labarai: Tsabar Rashin Adalci da Munafurci Ne Suka Hana Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Yin Magana Akan Abinda Fatima Ganduje tayi~Maryam Booth

March 24, 2018 0 Comments
Da take mayar da martani akan maganar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi na cewa hukumar Hisba bata da hurumin kama diyar gwamna akan shagalin da akayi a bikinta,
tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bayyana cewa, tsabar rashin adalci da munafurci ne suka sa malamin ya fadi haka.
Ta kara da cewa idan da ace 'yan fim ne suka yi wancan abu da an jishi da hujjoji kala-kala yana Allah wadai da su
Amma gashi yanzu diyar gwamna tayi yana tambayarsu wai ya suke so yayi.
Maryam ta kara da cewa idan be yi kame ba wannan ba matsala bace
amma irin yadda ya shafe kusan watanni yana sukar masu neman na kansu don rufawa kansu da iyalansu asiri wato 'yan Fim
ya kamata ace ya fito koda rana daya ne ko kuma ma awa daya yayi magana akan wannan lamari,
Maryam Booth ta kara da cewa su malaman da suka soki abinda diyar gwamnan tayi me ya faru dasu?,
Wato baza ka iya taba masu kudi ko mulki ba sai talakawa ko, don kada a sauke ka daga kujerar ka,
to ka sani komin daren dadewa ba zaka dawwama akan wannan kujera ba, bayan mulkinsu watarana sai ka sauka.
Maryam ta kara da cewa kana hada siyasa da addini, baka so ka batawa uban gidanka rai, to saika shirya abinda zaka gayawa Allah a ranar tashin kiyama, ka bar aikinka na dora mutane akan hanyar shiriya saboda siyasa.  
Secure Your Cargo
Manufacturers and suppliers of
tamper evident security seals acr
the African continent.
Robotic E

kannywood» KO Directors (John Woo) da (Aminu Saira) Basu Kai Gwamnatin Buhari Iya Shirya Film Ba. Inji Fati Muhammad

March 24, 2018 0 Comments
A yau ne gwamnatin shugaba muhammadu buhari ta karbi bakoncin yan matan dapchi da aka sace daga makaranta a cikin jahar adamawa,wannan gwamnati tayi iya kokarin ta na ganin ta ceto wannan yara daga hannun yan boko haram.
Amma ga abinda tsohuwar jarumar masana'antar Kanywood fati muhammad wanda itace Jakadiyar tsohun mataimakin shugaban kasa Atiku abubakar da ta ce.
"KO Directors (John Woo) da
(Aminu Saira) Basu Kai Gwamnatin Buhari Iya Shirya Film Ba..
.
Wannan Film Na 'Yan Matan dapchi
Yana kayatarwa
.
Muna Taya Iyayen Yaran Farin Cikin Dawo Musu Da Yaransu Kuma Allah Ya Kiyaye Mu Gaba Daya...
.
Shin Yaushe Za'a Kawo Karshen Film Din 'Yan Matan Chibok DYA Aka sace Koda Yake Baba dattijon Nan Da Baya Lefi Yace Acikin Kwana 100 Zai kwatosu har Yanzu Munji Shiru..
.
A MIKA MIN GAISUWA GA BABA BUHARI BABBAN DIRECTOR"

Thursday, March 15, 2018

kannywood» Zuwa Ga Masu Ganin Lefin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Akan abinda Fatima Ganduje Tayi - Fati muhammad

March 15, 2018 0 Comments
Don mallam baiyi magana ba akan Abinda FATEEMA GANDUJE tayi a wajen bikinta
Bai Kamata ku maida Abin siyasa ba domin ba SHIEK DAURAWA ne kadai Malami ba, kuma Ko yayi magana ko baiyi ba 'yan uwansa malamai sunyi. Kuma kada Wanda ya sake ganin lefin mallam
.
Idan kuna magana akan hukumar HIZBAH ne ai yanada wakilai
Domin nima 'YAR HIZBAH ce kuma na wakilci mallam nayi magana akan rashin dacewar abinda FATEEMA GANDUJE tayi.
.
Ahir dinku Mallam ba Sa'an yinku bane Wallahi duk wanda ya sake taba Muhibbar Mallam DAURAWA
zamu taba Muhibbar uban Mutum Kowaye!!
Tunda abin naku ya fara zama rashin mutumci

Wednesday, March 14, 2018

Kannywood: Majalisar Dinkin Duniya Ta karama Rahama Sadau

March 14, 2018 0 Comments
Fitacciyar Jarumar fina finan Kannywood da Nollywood Rahma Sadau ta sami lambar yabo a Birnin New York, a yayin da ake gudanar da bikin baje kolin fina finai na ‘Women Illuminated Film Festival’ wanda kungiyar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a ranar 12 ga watan Maris.

Bikin baje kolin fina finan na mata anyi shine tsawon awoyi 12, wannan biki dai anyi shine don haska mata masu shirin fina finai a fadin duniya da aka yi su kan karawa mata kwarin gwiwa, Fataucin mata, Auren wuri ga yara kanana, Ilimi da kuma Tabbatar da shari’a kan aldalci.

Ga jawabin ta
"I’ve been honored last night at the Women Illuminated Film Festival Parallel to United Nations.
I’m so privileged, delighted and very very PROUD to share the beautiful evening with so many incredibly amazing women. 🙌🏿
There are moments in life when you stop and ask yourself, how did I even get here? 🤔 Well this is definitely one of those moments I would cherish forever.
THANK YOU SO MUCH 🙏🏿@gwen_live @tess_cacciatore @vanessateemsma @unitednations @unwomen
#WomenIlluminatedFilmFestival #WomenEmpowerment #GirlChildMarriage #GirlPower #MakingADifference #Actress #GirlChildEducation
Tunic top from @trendyoutnet

Friday, February 16, 2018

KANNYWOOD LABARI ABIN DAKE FARUWA Na Fara Shiga Matsaloli Ne Tun Lokacin Da Na Fara Fitowa A Fina-finan Nollywood – Rahma Sadau

February 16, 2018 0 Comments
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood watau Rahama Sadau, ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata cewar, ta soma shiga matsalolin rayuwa ne tun bayan da ta fara fitowa a shire-shiren fina-finan kudancin kasar nan ta Najeriya da aka fi sani da Nollywood.
Jarumar dai wadda aka dakatar da ita daga fina-finan Hausa a shekarar 2016 ta bayyana yadda tace ta na shan bakar ukuba daga ‘yan uwan sana’ar ta na watau jaruman masana’antar Kannywood.
Jarumar ta kuma ce tabbas ba abu ne mai dadi ba kwata-kwata yadda ta ke shan tsangwama a wasu lokuttan idan mutun ya tsallaka zuwa shirin finafinai na kudanci ko na turawa musamman ma don dai yadda al’adu da dabi’u suka banbanta kawai.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa har yanzu dai jarumar na cikin dambarwa da jiran tsammani tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda ta shafe akalla watanni uku tana wani karatu yanzu kuma ta dawo gida tana jiran kungiyar su ta masu shirya fina-finan watau MOPPAN ta dake dakatarwar da ta yi mata.

Thursday, February 8, 2018

[Music] Nura M Inuwa “Mai Zamani Album” 2019 Intro

February 08, 2018 0 Comments
Assalam Sako Na Musamman Da Fitaccen Mawakin Fina Finan Hausa Nara M Inuwa
Game Da Sababbin Album's Ɗinsa Masu Zuwa A Shekara Mai Zuwa Masu Suna MAI ZAMANI Album da ANGO Album
Hausawa Dai Dama Sunce Ita Waƙa A Bakin Mai Shi Tafi Daɗi Gadai Sanarwar Daga Nura M Inuwa Kai Tsaye

NURA M INUWA

Assalamu alaikum warahmatulla hi ta'ala wabara katuhu, bayan sallama irin ta addinin musulunci,
ina yiwa ƴan uwa da masoya fatan alkhairi, kamar yadda aka saba barkan mu da shigo wa sabuwar shekara, alkhairan dake cikin ta Allah ya haɗa mu dashi, ya kuma tsare mu da dukkanin sharruka
Da wannan zanyi amfani wajan tallata muku sabbin Album's ɗina, wanda na sawa suna Mai Zamani, sabon Album ɗin Mai Zamani, yana ɗauke da darussa wanda bazan iya cewa komai a kansu ba
Kama daga kan faɗakarwa, nishaɗan tarwa, da kuma Soyayya, sai dai kun ji shi
fata na karku gajiya wajan jinkirin kawo muku sabbin Album's ɗina a kai a kai da banayi,
Sai na biyu kuma wanda na bashi suna ANGO Album, zanso kuji abinda yake ɗauke a cikin sa zasu zo muku ne a tare insha Allahu
Karda ku manta sunan su ANGO da Mai Zamani, tunani na gansuwar Ku, farin ciki na nishaɗin ku, ni ne naku-naku har kullum Nura M Inuwa

Monday, January 22, 2018

Wakokin Hip-Hop Za Su Danne Wakokin Hausa – G-BOY

January 22, 2018 1 Comments
Aminu Abdullahi wanda aka fi sani da Prince G-Boy matashin mawakin Hip-Hop ne a Jihar Kano, a tattunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa yana hangen nan ba da dadewa ba wakokn Hip-Hop za su danne dukkanin wakokin Hausa, sakamakon karbuwa da suka kara yi wajen jama’a. Haka kuma mawakin yay i kira ga mawakan da su rika tsaftacewa tare da zabar kalaman da za su. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Za mu so jin tarihin rayuwarka?
G-Boy: Sunana Aliyu Abdullahi Abdulhamid wanda aka fi sani da G-Boy a hakar wakokin Hip-Hop. An haife ni a unguwar Yalwa cikin Jihar Kano. Na yi karatun Firamarena a Makarantar Firamaren Yalwa a wannan makarantar na yi karamar sakandire. Bayan na gama sai na tafi babbar sakadire a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Dala inda na kammala a shekarar 2014. A yanzu haka ina kokarin gyara jarrabawata yadda zan sami damar ci gaba da karatuna duba da cewa sai da ilimi mutum za iya yin komai na rayuwa, koi ko ita harkar wakar ta fi tafiya idan mutum yana da ilimi.
Aminiya: Ya aka yi ka fara waka?
G-Boy: Zan iya cewa tun farko ni mai son wakoki ne don ina yawan saurarensu. Daga nan ne kuma ra’ayin yin wakar ya shige ni har ma na tsinci kaina da fara rubuta tare da rera wakoki. Zan iya cewa na fara rubuta waka a shekarar da na kammala makaranta wato a 2014. Da farko ina rubuta wakokin ne na rika rerawa a haka. Amma a yanzu a kwana a tashi na sami wadanda suke yi min recording wato double S inda nake gudanar da ayyukana a karkashinsu.
Aminiya: Wakoki nawa ka yi kuma mene ne jigon wakokinka?
G-Boy: Ina yin wakokin raf, sai dai a yanzu na fi yin R&B. Haka kuma idan ta kama ina yin wakokin nanaye. Abin da muke dubawa shi ne bukatar al’umma. Babu shakka na rubuta wakoki da dama wadanda ke ajiye da ba abuga ba za su kai 18. Sai dai a yanzu an buga wasu kamar su My mother da Lokacina da Me & You da Zo mu je da Let them know da sauransu. Amma idan zan lissafa har da wakokin da na yi tare da wasu jama’a wakokina za su kai 35. Duk da cewar ban riga an yi albam nawa na kaina ba, amma wakokina suna cikin albam din tarayya na abokan aikina. Amma in Allah Ya yarda a sabuwar shekara nan mai kamawa zan yi albam nawa na kaina. Zan iya cewa fadakarwa shi ne jigon wakokina, domin yawanicn wakokina ina yin su ne a kan wani abu da ke damun al’mma. Ita waka hanya ce mai sauki wajen isar da sako sakamakon sauraren waka da mutane key i, to idan mutum ana da wani abu da yake so ya fadakar da jama’a kai sai mu yi amfan da hanyar waka.misali abubuwa irinsu fyade da barace-barace da rashin ilimi da sauransu. A yanzu haka an saki wata sabukar wakata mai taken ‘BA MARAYA’ wacce ke nuni akan muhimamncin dogaro da kai.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga ’yan uwanka mawaka?
G-Boy: Ina kira ga ’yan uwana mawaka da mu daina amfani da damar waka muna bata tarbiyyar jama’a tare da yin zantuttuka wand aba su dace ba. mu sani cewa idan muka tsaftace harshenmu wajen fitar da kalamai masu kyau shi zai sanya al’umma su kara karbar wakokinmu. Haka kuma idan aka tsaftace kalmia, zai iya yiyuwa har a manyan makarantu za a rika yin nazarin irin wadannan wakokin. Ina ganin anan gaba wakokin Hip-Hop za su iya danne duk wasu wakoki na Hausa a fadin kasar nan.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati?
G-Boy: Ina kira ga gwamnati da ta taimaka mana duk da dai ana cewa idan ambu yay i yaw aba ya jin mai, amma dai yawanmu ba zai hana gwmanati ta taimaka mana ba. Sanin cewa a yanzu abubuwa ba su tafiya sai da kudi. Za ki tarar cewa idan mutum yana da basira yana kuma da kudi sai kika abubuwna suna tafiya daidai, sabanin wanda ke da basira ba shi da kudi. Muna bukatar gwamnai ta duba cewa mu muna samarwa da kanmu aikin yi ne ta hanyar yin waka, don haka muna bukatar ta tallafa mana. Haka kuma akwai bukatar ta rika ba mu kwarin gwiwa ta hanyar shirya mana tarurruka na bayar da lambar yabo wanda zai sa mu san gwamnati ta san da mu.

Sunday, January 14, 2018

[Music] Nura M Inuwa “Wasika Album” 2018 Intro

January 14, 2018 0 Comments
Talla : Nura M Inuwa Wasika Album And Manyan Mata Album.
Nura M Inuwa : Assalama Alaikuma Yan Uwah Masoya Da Abokan Arziki, Inai Mana Farin Cikin Sake Ganin Wannan Shekara Me Albarka,, Tare Da Fatan Allah Ya Sadamu Da Alkhairin Dake Cikinta.
Bayan Haka A Kokarin Da Nake Na Sakar Muku Album Biyu A Shekara Yauma Nazo Muku Da Wani Salo Mai Kwantar Da Hankali Wanda Zai Saku Kaguwa Da San Kuji Kundin Da Na Sawa Suna Wasika.
Wasika Wani Album Wanda Na Dade Banyi Irin Saba Musamman A Bangaran Da Aka Sanni Na Wakoki Irin Na Soyayya Masu Daga Hankali A Wani Bangaran Kuma Su Kwantar Da Hankali.
Kundin Album Din Wasika Zai Dada Koya Mana Yadda Ake Hakuri Yayin Da Masoyi Ya Rasa Abinda Yake Kauna.
Haka Kuma Kamar Yadda Aka Saba Bashi Kadai Bane Hade Yake Da Album Dinda Nasa Mishi Manyan Mata Album.
Shima Album Din Manyan Mata Na Shirya Shine Domin Nuna Matsayi Martaba Da Kuma Kima Irin Na Mata Da Sannu Zasu Zo Muku A Tare Shekara Mai Zuwa.
Daga Daku Masoyin Ku Mai Alfahari Daku Nura M Inuwa.

[Music] Sabon Album Hamisu Breaker “Dalilin So Album”

January 14, 2018 0 Comments
[Music] Hamisu Breaker “Dalilin So Album” 2018 New Album
Albishirin ku ma'abota ji gami da sauraron wakokin Hausa na zamani!
Muna farin cikin sanar daku cewa, daya daga cikin fitattun mawakan Fina-finan Hausar nan dan asalin garin Kano a tarayyar Nigeria wanda ake yiwa lakabi da Breakan Waka ko kuma, Hamisu Breaker
Yana mai yi muku albishir da sabon Album dinsa da zai fitar kwanan nan, mai suna DALILIN SO ALBUM
Wanda ya kunshi Zafafan wakoki masu mutukar dadin Sauraro, nishadantar wa, tare da sanyaya zuciyar ma'abota Sauraro
Inda Album ke dauke da dadadan wakoki har guda Goma Sha Hudu, gasu kamar haka
1= Ina Da Masoyiya
2= Mai Sona
3= Tamburan Masoya
4= Dalilin So
5= Ga Hannuna
6= Budurwa ta

7= Wasika

8= Tanadin So

9= Kama Muke

10= Ni Naki Ne

11= Zo Da Farin Ciki

12= Dani Dake

13= Kibiyar Ajali

14= Amarya Gamu


Album din yana nan fitowa nan bada jimawa ba, maza ku hanzarta ku nemeshi ta hanyar data dace karda ku bari a baku labarii

Tuesday, January 2, 2018

Malaman Addini Na Samun Salon Wa’azin Su Ne Daga Fina-finan Mu – Rashida Lobbo

January 02, 2018 0 Comments
Wata sabuwar jarumar Kannywood da wasu masu fashin baki ke cewa ta shigo masana’antar da kafar dama tayi ikirarin cewa malaman addini suna samun salon yadda za su yi wa’azin su ne daga fina – finan hausa.Rashida Lobbo dai tana daya daga cikin jaruman da suka karbi kyauta a bikin karama jaruman fim da mujalar city people ta shirya kwanakin baya a jihar Lagos.
Rashida Lobbo wacce ake wa lakabi da yar Yola tana cikin sabbin jarumai da tauraronsu ke haskawa kuma da alama ta shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar cikin shekarar 2018 da zamu shiga.
Kamar yadda ta bayyana a shafin ta na sada zumunta na facebook, jarumar tana karkashin kamfanin shirya fina-fina na FKD wato mallakar shahararen jarumi, Ali Nuhu

Monday, November 20, 2017

Ali Nuhu ba Ubangida na bane, Uba na ne – Adam Zango

November 20, 2017 0 Comments
Adam Zango ya fadi a shafin sa na Instagram cewa ba kamar yadda ake masa ganin cewa ba sa ga maciji da Ali Nuhu, matsayin Ali yafi na ubangida.
” Ali ba ubangida na bane Ali Uba ne a gareni.
A makon da ya gabata Adam Zango ya fito yana nuna fushin sa ga wasu abubuwa da bai fadi ko menene ba da wasu ke yi masa a farfajiyar finafinan Hausa na Kannywood, inda ya ce yanzu ya kai makura duk Wanda ya ce masa cas zai ce masa Kyle.

Tuesday, November 14, 2017

Dandalin Kannywood: Dalilin da yasa bana sanya kananan kaya - Jaruma Aisha Tsamiya

November 14, 2017 0 Comments
Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar asalin jihar Kano mai suna A'isha Aliyu da ake yi wa lakani da A'isha Tsamiya ta fito ta bayyanawa duniya babban dalilin da ya sanya ita bata saka kananan kaya kamar sauran wasu jaruman.
Jarumar dai ta bayyana cewa ita ba ta sa kananan kaya ne musamman saboda dalilin cewa ba sa yi mata kyau idan ta sa su don kuma ta dan gwada a lokutan baya.
Majiyarmu dai ta samu cewa wasu da daga cikin jarumai mata a masana'antar fim din kan sanya kananan kaya a yanayin rayuwar su ta yau-da-kullum ko kuma ma a cikin fim amma ba'a taba ganin ita A'isha Tsamiya din ba da su.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai mun kawo maku labarin yadda wata kungiya a arewacin kasar nan tayi kira ga matan yankin da suyi koyi da dabi'un jarumar fim din Rahma Sadau wanda kuma hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin mata da maza a yankin inda suke ganin hakan bai dace ba.

Sunday, November 12, 2017

Dalilin da ya sa na kirkiro shirin ‘Taurarin Zamani’ – Ofime

November 12, 2017 0 Comments




Dan Najeriya mazaunin kasar Kanada, kuma mai shirya fina-finai, Rogers Ofime ya bayyana cewa kamfaninsa mai suna Natibe Media ya kirkiron shirin talabijin mai suna ‘Taurarin Zamani’ ne don ya nuna arewacin Najeriya ga duniya.
Rogers Ofime wanda kuma darakta, wanda ya shirya manyan fina-finan Turanci na Nollywood irinsu ‘Price of Spice’ da kuma ‘Olaibiri’ ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Jos Daraktan ya ce, shirin Taurarin Zamani zai nuna manya masu fada a ji da ke Arewacin Najeriya.

Ya ce, “Mun samu damar tattaunawa da manyan masu fada a ji ’yan Arewa, wadanda suka yi fice a bangarori da dama da suka hada da siyasa da aikin gwamnati da kasuwanci da kuma fitattu a bangaren waka da kida da kuma masana’antar fina-finan hausa ta Kannywood.” Ya kara da cewa a bangaren nishadi sun tattauna da Ali Nuhu da Rahama Sadau da mawaki Umar M Shareef da jarumi Sadik Daba da Yakubu Muhammad da Sani Danja da mawaki Ahmad Mai Shanawa da Classik da sauransu. Fitaccen Furodusa kuma jarumin fina-finan Hausa, Usman Uzee ne yake gabatar da shirin, inda ya kuma tattauana da fitattun mutane irinsu Jerry Gana da Sarah Jibril da Zainab Bagudu da Halima Idris da kuma Hon. Munirat Suleiman.

Sauran wadanda suka bakunci shirin sun hada da Husseini Coomasie da Sanata Nenadi Usman da Hon. Aminu Goro da Isaac Dabid Balami da sauransu.
Ya bayyana cewa tuni aka fara nuna shirin ‘Taurarin Zamani a tashar Hausa ta Africa Magic a ranar Asabar da misalin 5:30 na yamma da kuma maimaici a ranar Lahadi da misalin 5:30 na yamma.

Ofime wanda ya shirya fina-finan da ake nunawa a talabijin da suka hada da ‘Tinsel’ da ‘The Johnson’ ya ce an kuma fara nuna shirin a gidan Talabijin na Liberty.

Tuesday, November 7, 2017

Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai

November 07, 2017 0 Comments
Wani hoton da ya bulla a dandalin zumunta a satin da ya gabata na ci gaba da daukar hankulan jama'a da dama na Jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa Halima Atete da kuma tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a filin jirgi. Hoton dai na kunshe ne da jarumar zaune a kusa da shahararren dan siyasar inda ta dora wata jar hula da ke nuna alamun mubayi'a ga bin tafarkin Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon Gwamnan. NAIJ.com dai ta samu daga majiyoyi da dama cewa an dauki hoton ne a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a garin Dubai a dunkulalliyar Daular Larabawa. Da ma dai ba tun yauba jaruman dake shirya fina-finai a jihar ta Kano din suna nuna matukar kaunar su ga tsohon Gwamnan da suke kallon yana maraba da sana'ar ta su.
Source-: NaijHausa

Monday, November 6, 2017

Nafisa Abdullahi ta gagara a Kannywood, ta lashe gagarumar kyauta a birnin Landan

November 06, 2017 0 Comments
Nafisa Abdullahi ta yi zarra a Kannywood
- Nafisa Abdullahi ta lashe kyautar gwarzuwar Hausa Fim na shekarar 2017
- Ali Nuhu, Ramadan Booth sun halarci taron a Landan
Fitacciyar jarumar wasan Hausa Fim, Nafisa Abdullahi ta lashe kyautar gwarzuwar Hausa Fim na shekarar 2017 a bikin bada kyautuka na finafinan Afirka daya gudana a kasar Ingila.
An gudanar da wannan gagarumin biki ne a ranar Asabar, a birnin Landan, inda daga cikin wadanda suka halarci bikin karramawar har da Ali Nuhu da Ramadan Booth, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ita ma jarumar tayi farin ciki sosai, inda ta bayyana hakan a shafin Twitter.
KU KARANTA: 2019: Matuƙar Buhari ba zai tsaya takara ba, toh ni zan tsaya – Yariman Bakura
Nafisa ta taka rawar gani a wasu fina finan Kannywood da suka hada da ‘Guguwar So’, ‘Dan marayan Zaki’ da ‘Ya daga Allah.’, kuma ta yaba da amsar wannan kyauta, duk da dai ba shi ne na farko ko na biyu ba, inji ta.
Nafisa Abdullahi
“Dayake dai wannan kyautr ba itace ta farko, ko na biyu, ko na uku a waje na ba, amma dai nayi matukar farin cikin (African Film Awards). Na sadaukar da shi ga duk wadanda suka taimaka min.”
In ji ta.


Nafisa tare da Ali Nuhu a Stamford Bridge
Daga karshe ta gode ma masoyanta, saboda goyon bayan da suke bata a kullu yaumin, sa'annan tare da ALi Nuhu suka garzaya filin wasan Chelsea na Stamford Bridge, inda suka kalli wasan Chelsea da Manchester.

Saturday, November 4, 2017

Jarumar Finafinan Hausa da tafi kowace jaruma karfi: Sha'awanatu Muhammad

November 04, 2017 0 Comments
Muhammad kenan dauke da irin karfennan da karfafan maza(cikin mazan ma ba kowa bane zai iya dagawa ba) ke dagawa dan motsa jiki, gaskiya ta cancanci a bata kyautar karramawa a matsayin jaruma mace mafi karfi a masana'antar finafinan Hausa dan na tabbata Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, Fati Washa duk ba za su iya daga wannan karfe ba. Kai koda cikin jarumai maza ba kowane zai iyawa wannan karfen zuwa daya ba ya dagashi.

Kannywood: Rigima Tsakanin Rahama Sadau Da Jarumi Ali Nuhu Ta Barke

November 04, 2017 0 Comments
Daga Mikiya
Binciken da muka yi ya nuna mana cewa tsskanin Magoya bayan Jarumi Ali Nuhu Dana Rahama Sadau suna Ruwan Ashariya Tsakaninsu
Talla
su dai magoya bayan Ali Nuhu mohammed suna hakan ne domin
zargin jarumar da yi wa ogan na su zagon kasa.
anda a ganin su ita
jarumar tana yin zagon kasan ne don anki a sanyata a cikin jerin jaruman
da za su fito a fim din FKD na gaba
mai suna ABOTA, sai aka sanya
wadda basu shiri da ita wato Nafisa
Abdullahi.
Wata majiya ta tabbatar mana da cewa tuni dai duk wani makusancin Ali Nuhu da mukarrabansa a ka
sanyasu su ka yi ‘Unfollowing’ din
Rahama Sadau a shafin su
Instagram.
Yanzu haka dai magoyan bayan Ali Nuhu sun sanya damarar Rigima da Jarumar a shafukan su na yanar gizo. Ga kadan daga cikin rubututtukan
wasu:
“Wallahi duk wanda ya taba Ali Nuhu
sai Inda karfina ya kare, an yi walkiya
mun ganki Kin manta lokacin da kike cikin
wahala aka fito da ke a cikin mutane” Kin manta lokacin da aka fifitaki akan kowa? Kin manta lokacin da
wulakantaki shi din da kike Zagi ya
rufa maki asiri?
“To, Wallahi ki shiga taitayinki, ki kuka da kanki. Don wallahi muna
jiranki sai kin maimaita duk abin da
kika fadi. Kuma kin yi kan ki kar ki kara cewa
shi babanki ne shi wawuya…
KORARRIYA
Ga kuma Abunda magoya bayan
Rahamar suka Rubuta kamar haka suna cewa dan Allah yai ma ni’ima , ya
Daukaka, tilas sae kayi hkuri da wayanda za suyi mk hassada, da
sharri dan dae sucinma gurinsu. Kiyi hkuri da ZAGI, BAKAR MAGANA,
ko CIN ZARAFI a boye ko a sarari ko
ta social media da ake yi. Rahama sadau Karki rama zagi idan an yi miki, domin in baki ramaba mai zagin iyayensa ya zaga.
Kisani Idan Jama’a zasu taru domin su amfanar da ke wani abu a duniya, wlh baza su amfanar da ke komai ba
sai abin da Allah ya tsara a gareki. Haka da Jama’a zasu hadu domin su cutar da Ke ko suga kin walaqnta wlh baza su iya yin ko daya ba, sai abin da Allah ya tsara a kanki
Karki kalli magulmata, Aikinsu suke yi, Ba ke ki ka basu aikin ba ”
me zakuce?