Follow Us @soratemplates

Showing posts with label Labarin wasani. Show all posts
Showing posts with label Labarin wasani. Show all posts

Monday, April 23, 2018

Labaran wasanni : Barcelona ta dauki Copa del Rey bayan lallasa Sevilla 5-0

April 23, 2018 0 Comments
Barcelona ta dauki kofin Copa del Rey karo na hudu a jere bayan da ta lallasa Sevilla da ci 5-0, ranar Asabar, a filin Atletico Madrid, Wanda Metropolitano.
Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci Barcelona ta ci 3-0, inda Luis Suarez ya fara daga raga a minti na 14, bayan da Philippe Coutinho ya saka masa kwallon.
Lionel Messi ne ya zura ta biyu, kuma bal dinsa ta 40 da ya ci wa kungiyar a bana a minti na 31 da fara wasa.
Suarez ya kara ta uku bayan da Messi ya saita masa bal din ana saura minti biyar a tafi hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 52 Andres Iniesta ya ci bal ta hudu, kafin kuma Philippe Coutinho ya ci ta biyar da bugun fanareti, wand hakan ya sa Barcelona daukar kofinta na farko tun lokacin da kociynta Ernesto Valverde ya kama aiki a watan Mayu.
Sevilla wadda ta doke Atletico Madrid ta samu gurbin wasan na dab da na karshe ba ta yi wani katabus ba a wasan da Barcelona ta mamaye a filin Atletico na Wanda Metropolitano.
Barcelona za ta iya daukar kofi na biyu inda za ta daga na La Liga a ranar Lahadi, idan ta biyu a tebur Atletico Madrid ta sha kashi a hannun Real Betis, a karawar da za su yi da karfe 7:45 na dare agogon Najeriya.
A haduwa tara da suka yi a karshen nan Sevilla ba ta taba doke Barcelona ba, kuma rabonta da cin wasa tun bayan da ta fitar da Manchester United daga gasar kofin zakarun Turai, ranar 13 ga watan Maris.

Tuesday, November 14, 2017

Man United za ta dauki Asensio na Madrid

November 14, 2017 0 Comments
Manchester United na shirin daukar Marco Asensio, za kuma ta ba shi yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar, in ji wani rahoto daga Spaniya. Kocin United, Jose Mourinho na neman 'yan wasan da za su kara masa karfin kungiyar a watan Janairu da wadanda za su buga masa tamaula a badi a Old Traford. Jaridar Don Balon ta ce United za ta bai wa mai wasan tsakiya na Real Madrid fam miliyan 177 idan har ya amince zai koma buga gasar Premier. Dan wasan mai shekara 21, yana da yarjejeniya da Real Madrid har zuwa kakar 2023, ya kuma ci kwallo hudu ya kuma taimaka aka zura biyu a raga a wasa takwas da aka fara da shi. Sai dai kuma Isco na kokarin kwantar wa da Asensio hankali kan rade-radin da ake yi a kan dan kwallon.

Monday, November 6, 2017

Real Madrid ta huce haushinta a kan Las Palmas

November 06, 2017 0 Comments


Marco Asensio ya ci daya daga cikin kwallaye mafi bajinta a gasar La Liga ta bana, yayin da kungiyarsa Real Madrid ta wartsake daga kayen da ta sha a hannun Tottenham, inda ta buge Las Palmas.
Zuwa yanzu Real ba ta nuna bajintar da ta kai ta bara ba, wadda ta sanya ta yin karko, sai dai wasansu na ranar Lahadi ya fi wanda suka yi cikin tsakiyar makon jiya.
Cin da Casemiro ya yi da ka ne, ya sa Real Madrid ta yi wa abokiyar karawarta zarra, kafin Asensio ya dirka kwallon da ta kwantar da hankalin kungiyar daga ratar yadi 30.

Sai kwallon da Isco ya cafa, wadda ta kammale nasarar Real.
An ga Cristiano Ronaldo, wanda ya sa kwallon da aka ci ta uku, ya harzuka a cikin fili saboda karancin damammakin cin kwallon da ya samu, ko da yake, ya je daf da gola Raul Lizoain inda ya dankara kwallon da ta bude tsawon inci da dama ta fita.

Real Madrid ta yi kokarin kai hari sau 14 a farkon rabin lokaci, sai dai ba ta ci kwallo ba sai wadda Casemiro ya sa wa kai bayan an kwaso kwanar da Jonathan Calleri cikin rashin sani ya goga.
Yanzu dai kungiyar ce ta uku a kan tebur, inda suke kai da kai wajen maki da ta hudu Atletico Madrid, kuma jagorar gasar, Barcelona mai maki 31 ta ba ta ratar maki takwas.

Friday, September 29, 2017

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure

September 29, 2017 0 Comments


Babban Dan wasan nan Ronaldo na shirin yin aure
Ronaldo zai auri Budurwar sa Georgina Rodriguez
– A shekara mai zuwa ne ‘Dan wasan zai zama Ango
Ana dai sa rai babban Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya shiga daga ciki a badi kamar yadda labari yake zuwa mana.
<script async src=

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" class="article-image__picture" height="640" src="https://i.onthe.io/vllkyt6d6e62tlbcf.afcc316d.jpg" style="border: 0px; display: block; height: auto; margin: 0px auto; max-width: 100%; padding: 0px;" title=
"Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" width="960" />
Cristiano Ronaldo zai auri Budurwar sa
Tauraron Dan wasan na Real Madrid Cristiano Ronaldo zai auri budurwar sa Georgina Rodriguez a shekara mai zuwa ko da dai har yau ba a san takamamen ranar ba. Yanzu haka dai Rodriguez mai shekaru 23 ta na da cikin ‘dan Ronaldo.
KU KARANTA: An kama wasu da ke yaudarar mata a Turai
<script async src=

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" class="article-image__picture" height="492" src="https://i.onthe.io/vllkyt7tc9b9413qv.c4d2bf41.jpg" style="border: 0px; display: block; height: auto; margin: 0px auto; max-width: 100%; padding: 0px;" title="Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure" width="820" />

Cristiano Ronaldo da iyalin sa a gida

Jaridar Correio de Manha tace Dan wasan dai ya ba Budurwar ta sa zobe mai tsada har na fam miliyan Euro £232,000 wanda ya kai kusan Naira Miliyan 100. Kwanan nan ne aka ga Rodriguez ta shiga Makarantar koyon rawa a Sifen.
Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve kwanakin baya, haka kuma dama dai yana da yaro mai shekaru 6 a Duniya. Ko da yake dai har yanzu Dan wasan bai tabbatar da ainihin iyayen yaran ba.

Thursday, September 28, 2017

Zakarun Turai: Chelsea ta kafa tarihi bayan doke Atletico 2-1

September 28, 2017 0 Comments
Chelsea ta bi Atletico Madrid har gida ta doke ta da ci 2-1 a wasansu na kofin zakarun Turai na rukuni na uku (Group C), a ranar Laraba.
Minti 40 da fara wasa Antoine Griezmann ya ci Chelsea da fanareti, bayan da David Luiz ya rike Lucas Hernandez lokacin da aka yo wani bugun gefe.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 59 sai Morata, wanda Chelsea ta sayo daga Real Madrid ya rama mata kwallon, kafin kuma a dakika ta kusan karshen wasan Michy Batshuayi ya ci wa Blues din ta biyu.
Nasarar da Batshuayi wanda ya shigo wasan daga baya, ya sa Chelsean ta samu ta zo ne bayan damar da Cesc Fabregas da Morata suka barar.
Yanzu Chelsea ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta bi Atletico gida ta doke ta, kuma hakan ya kasance rashin nasara na farko a gasar Turai da kungiyar ta Spaniya ta yi a sabon filin wasanta.
Sannan hakan ya kawo karshen wasa 11 da Atletico wadda ta je wasan karshe biyu a shekara hudu da ta wuce ta gasar, ta yi ba tare da an doke ta ba a gida a gasar kofin na zakarun Turai.
Wannan shi ne karo na biyu da Atletico ta sha kashi a karkashin kociyanta Diego Simeone a wasa 24 na kofin zakarun Turai a gida.
Nasarar ta sa Chelsea ci gaba da kasancewa ta daya a rukunin (Group C) da maki shida, biyu kenan tsakaninta da Roma, sannan kuma biyar tsakaninta da ta uku Atleticon.
Sakamakon sauran wasannin na zakarun Turai na Laraba;
FK Qaraba 1- 2 Rom
Paris SG3-0 Bayern Mun
Anderlech 0- 3 Celtic
Juventus2- 0 Olympiakos
Sporting 0- 1 Barcelona

Wednesday, September 6, 2017

Dan wasan Real Madrid Ronaldo zai kara samun yaro kwanan nan

September 06, 2017 0 Comments
Dan wasan Real Madrid Ronaldo zai kara samun yaro kwanan nan
- Ba mamaki kwanan nan Budurwar babban Dan wasan ta sauka
- Tun kwanakin baya Cristiano Ronaldo ya tabbatar da juna biyun
Mun fahimci cewa gwarzon Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo zai kara samun yaro kwanan nan.
Cristiano Ronaldo na shirin samun wata karuwa
Ronaldo na shirin samun karuwa
Babban Dan wasan gaban Duniya Ronaldo na daf da zama uba karo na 4 a Duniya da zarar Budurwar sa Georgina Rodriguez ta sauka. Wannan ne dai karo na farko da wata Budurwar Dan wasan za ta haihu bayan ya samu 'ya 'ya 3 wanda har yau ba a san Mahaifan su ba.
Cristiano Ronaldo zai kara samun jariri kwanan nan
Budurwar Cristiano Ronaldo tana da ciki
Hoto daga GoffPhotos
Tun a watan Yuli Dan wasan ya tabbatar da cewa Budurwar ta sa na da juna biyu kuma ba mamaki yanzu ta kusa sauka. Yanzu dai akalla an dauki kusan shekara guda kenan Ronaldo yana tare da Rodriguez wanda ta ke aiki a Kamfanin Gucci.
Babban Dan wasan yana da 'ya 'ya 3 yanzu wanda babban yake da shekaru 7 sannan kuma ya samu tagwaye kwanan nan. Dan wasan yace yadda yake goya lamba 7 haka yake so ya goya 'ya 'ya 7.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a 
Adaadakawa@gmail.com

Friday, August 11, 2017

Ina son tashi daga Liverpool daga dan wasanta Mai tashe wato countiho

August 11, 2017 0 Comments
Dan wasan kungiyar Liverpool Philippe Coutinho ya bayyana bukatar barin kungiyar, bayan kulob din ya fitar da wata sanarwa wadda a ciki ta ce dan wasan ba na sayarwa ba ne.
Coutinho ya bayyana aniyyarsa ta barin kungiyar ne a wata wasikar e-mail. Sai dai kungiyar da yi watsi da bukatarsa.
Liverpool ta ce dan wasan tsakiyarta na kasar Brazil Philippe Coutinho "tabbas" ba na sayarwa ne.
A ranar Laraba ce, kungiyar ta ce a kai kasuwa ga tayin yuro miliyan 100 da Barcelona sake yi wa dan wasan mai shekara 25.
Tayin Barca na farko, wanda nan take Liverpool ta ce albarka, ya kunshi biyan kusan yuro miliyan 77, da karin yuro miliyan 13 da rabi a kai.
A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, masu mallakar kungiyar, Fenway Sports Group, sun ce, "matsayin tsayin dakan" da suka yi, shi ne "babu wani tayi da zai ja hankalinmu".
Liverpool ta kara da cewa: "Philippe zai ci gaba da zama a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool har bayan rufe kasuwar 'yan wasa ta bazara."
Da yake jawabi a wani taron manema labarai gabanin fara karawa ranar Asabar a gasar Firimiyar Ingila a Watford, kocin kungiyar Jurgen Klopp ya ce Coutinho ba zai buga wasan Liverpool na farko ba saboda matsalar ciwon baya.
Klopp ya kuma bayyana tantama kan bayyanarsa a wasan samun cancantar shiga Gasar Zakarun Turai zagayen farko da Liverpool za ta yi ranar Talata a Hoffenheim don kuwa Coutinho "bai yi atisaye ba tun ranar Juma'a a makon jiya".
Coutinho, wanda ya ci kwallo 14 a dukkan gasannin da ya buga a kakar da ta wuce, ya sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar shekara biyar a watan Janairu, wadda ba ta kunshi shadarar fitarsa ba. A shekara ta 2013 ne dan wasan ya shiga Liverpool a kan yuro miliyan 8 da rabi daga Inter Milan.
Haka zalika, an ki sallama wa Barcelona tayin da ta yi wa dan wasan gaba na Borussia Dortmund Ousmane Dembele, tun bayan sayar da dan wasan gaba na Brazil Neymar a kan kudi mafi tsada na yuro miliyan 200 ga Paris St-Germain cikin makon jiya.

Thursday, August 3, 2017

Zan koma PSG inji Neymar

August 03, 2017 0 Comments
Shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona ya sanar da kungiyar cewa yana so ya bar kungiyar zuwa kungiyar kwallon kafa ta PSG dake kasar Faransa.
Ko da yake Neymar na da kullalliyar alkawari tsakanin sa da Barcelona cewa duk wanda zai siye shi sai ya biya kudin da ya kai Euro miliyan 222 kafin a yarda a siyar da shi.
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce a shirye take ta biya wadannan kudade da aka sa kan Neymar.
Yanzu dai aski ya zo gaban gashi domin ko a karisa ne ko a barshi haka babu kyan gani.
Bayanai sun nuna cewa mahaifin Neymar ya gama tattaunawar kuma shi kanshi dan kwallon ya nuna cewa yana son ya koma PSG din.

Wednesday, July 26, 2017

Real Madrid itace ta daya a duniya wajansiya dan wasa mafi tsada a duniya

July 26, 2017 0 Comments
Real Madrid ta shirya sayen Kylian Mbappe kan kudi Yuro miliyan 180 daga Monaco a bana in ji jaridar Marca.
A labarin da ta wallafa ta ce wannan kudin da Madrid za ta biya Monaco zai haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a 2016.
Madrid din za ta fara biyan Monaco Yuro miliyan 160 daga baya ta karasa biyan Yuro miliyan 20 da sauran tsarabe-tsaraben da zai saka hannu kan yarjejeniya.
Ana taya Mbappe ta bayan gida - Monaco
Jaridar ta ce da PSG ta dauki Neymar kan Yuro miliyan 222 daga Barcelona wanda ya ce zai ci gaba da zama a Nou Camp, da shi ne zai zama mafi tsada a banar.
Wannan kuma ba shi ne karon farko da Real Madrid ke sayan 'yan kwallo mafi tsada a duniya ba.

Thursday, July 13, 2017

Labari da dumi duminsa

July 13, 2017 0 Comments
Audu Ogbeh ya kai wani ziyara ga Gwamanan jihar Osun Aregbesola

- Ya ce ya kai ziyarar ne domin karfafa alakar dake tsakanin ma’aikatar noma da jihar

- Ya ce shigo da shinkafa ya kusa zuwa karshe a watan Disamba

Cif Audu Ogbeh wanda ya kasance ministan noma da kuma ci gaban kakkara ya bayyana cewa Najeriya zata daina shigo da shinkafa a Disamba.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ministan ya yi magana ne a Osogbo, babban birnin jihar Osun a lokacin da ya kai ziyara ga Ogbeni Rauf Aregbesola, gwamnan jihar, ziyarar ban girma.

Ogbeh ya ce Najeriya zata dukufa gurin samar da shinkafa mai yawa , amma abun bakin ciki ne cewa Najeriya na kashe biliyoyin dala gurin shigo da abinci.
Bestarewa.com.ng

Najeriya zata daina shigo da abinci kwanan nan inji Ogbeh

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a KadunaHukumar EFCC tayi ram da wani Bawan Allah a Kaduna

Ya ce ma’aikatar noma ta sake fasalin al’amura domin ta samar da wadataccen abinci ga Najeriya.

Ya ce ya kai ziyarar ne domin karfafa alakar dake tsakanin ma’aikatar noma da jihar.

A halin yanzu, gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara rabon kayayyakin abingi ga kauyuka a karamar hukumar Ran Kala Balge dake jihar Borno.

Sunday, July 9, 2017

Sabon dan kwallo da Real Madrid suke nema

July 09, 2017 0 Comments
Real Madrid ta sanar cewar a ranar Juma'a za ta gabatar Jesus Vallejo ga magoya bayanta a Santiago Bernabeu.
Kuma wannan ne karon farko da dan kwallon mai tsaron baya mai shekara 19 zai saka rigar kungiyar ya kuma taka filin wasa.
Madrid ta sayi Vallejo daga Zaragoza a shekarar 2015, amma ta amince ya ci gaba da taka-leda a can a matsayin aro inda ya buga wasa 20.
A kakar 2016/17 Madrid ta bai wa Eintracht Frankfurt aron Vallejo, inda ya buga wasa 25 a gasar Bundesliga da aka kammala.
Vallejo dan kwallon tawagar matasa ta Spaniya shi ne ake hasashen zai maye gurbin Sergio Ramos a nan gaba kadan.
Da zarar Madrid ta gabatar da dan kwallon a gaban magoya baya, za kuma ta bai wa 'yan jarida damar yi masa tambayoyi.

Labarin wasani

July 09, 2017 0 Comments
Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta garin Bauchi ta ci Kano Pillars 2-0 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na 28 da suka fafata a ranar Lahadi.
Wikki ta fara cin kwallo ta hannun Ahmed Usman a minti na 10 da fara tamaula, bayan da aka dawo ne daga hutu ta kata ta biyu ta hannun Chinedu Onyelonu.
Da wannan sakamakon Wikki Tourist ta ci wasanninta takwas da ta buga a jere a gida a kwanan nan.
Ga sakamakon wasu karawar da aka yi a gasar ta Firimiyar Nigeria:

Rangers 1-1 3SC

Katsina 2-1 Lobi

Enyimba 3-0 Tornadoes

Plateau Utd 3-0 Akwa Utd

Gombe Utd 2-0 El-Kanemi

Abia Warriors 2-0 Nasarawa Utd

ABS 2-4 Sunshine Stars


Labarai masu alaka