Babban sakataren kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta cewa yana yawan ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi a cikin wa'azinsa.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa BBC a ofishinmu da ke Landan a makon daya gabata, inda ya ce shi a tarihin rayuwarsa bai taba ambaton sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba a cikin wa'azinsa.
Malamin addinin ya ce, "idan akwai wanda ke da wani kaset na wa'azinsa da ya ambaci sunan malamin, to kofa a bude take ya fiddo da shi ya yada wa duniya."
Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.
"Hasali ma shi shaihin shi ke ma ambatarmu a cikin wa'azinsa, domin ya kira sunana dana mahaifina ba sau daya ba, ya kuma kira shugaban kungiyarmu da sunansa karara, har ma ya kan siffantashi da munanan siffofi wanda shi shugaban bai taba mayar masa da martani a kan hakan ba," in ji shi.
Jagoran Izalan ya ce "ita da'awa ta ahlul sunnah ba da'awa ce ta kiran sunaye ba."
Thursday, November 30, 2017
(video) Ban taba ambaton Sheikh Dahiru Bauchi a wa'azina ba — Kabiru Gombe
by
Bestarewa
on
November 30, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment