Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)
Hajara ta fara aiki a matsayin jami’ar soja a 1986. Ta samu daukaka inda ta kasance bahaushiya kuma musulma ta farko daga yankin arewa da ta fara kai wa matsayin kwamanda, wanda yayi daidai da matsayin kanal a soja. Hajara, yar marigayi Marafan Birnin Kudu, Kanall Bashari Umaru daga Birnin Kudu a jihar Jigawa, yanzu ita ce shugaban ma’Ć”ikatan jinya na asibitin sojoji dake Kano. Ta taba zuwa yaki a Congo, daga cikin wuraren da tayi aiki akwai Ibadan da Kaduna. An haife ta ne a Dorayi Quarters a ranar 19 ga watan Maris, 1964, ta girma ne a Yakasai Quarters a Kano, sannan ta fara karatun firamare a Wagwarwa Primary School, sannan ta koma St. Louis Primary School.
R ead more: Shugaba Buhari ya kashe zama da Ministocin sa na yau
Kasancewarta daliba mai ilimi, Hajara ta samu shiga Queen’s College, Lagos da St. Louis Secondary School, Kano. Ta zabi karatu a Kano ne saboda sauyin aikin da mahaifinta ya samu zuwa Kano. Bayan ta kammala da karatun sakandare ne ta shiga makarantan koyon jinya a Kano.
A cikin makarantan ne ta yanke shawarar shiga aikin sojojin sama wanda ya biyo bayan neman kwasan ma’aikatan kula da lafiya.
‘’Babu shakka hakan ya kasance abun al’Ć”jabi. Mahaifiyata bata so hakan ba ko kadan. Mahaifina ya amince ne kawai domin faranta mun rai. Amman ya karfafa mun gwiwa, ya kuma girmama zabin da nayi." Inji ta.
Wednesday, August 23, 2017
Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)
by
Bestarewa
on
August 23, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment