'Yan sanda sun kama mutum 12 bayan harin birnin Landan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai ya kuma jikkata wasu 48.
An kama mutanen ne a garin Barking da ke gabashin Landan bayan wani samame da 'yan sandan suka kai gidan daya daga ciki mahara ukun da suka kai harin.
Wata farar mota ce ta ture wadansu mutane da suke tafiya a ƙafa a kan gadar birnin Landan da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar.
Daga nan ne sai wasu mutum uku suka fito daga motar kuma suka fara daɓawa mutane wuƙa a kusa da kasuwar Borough Market. Sai dai 'yan sanda sun harbe su bayan mintuna kadan.
Yayin da take Allah-wadai da harin, Farai Ministar Birtaniya ta ce "lokaci ya yi da za mu ce ya isa haka"
Har ila yau, an gano wasu abubuwan fashewa a wani gida da 'yan sanda suka kai samame a garin Barking ranar Lahadi da safe.
Ɗaya daga cikin maharan da aka kashe ya kwashe shekara uku a gidan kuma yana da mata da 'ya'ya biyu, kamar yadda maƙwabtarsa suka bayyana.
Wannan ne hari na uku da aka kai Birtaniya a cikin wata uku, harin yana zuwa ne bayan harin da aka kai a gadar Westminster a watan Maris, wanda ya kashe mutum biyar, sai kuma harin Manchester kimanin makonni biyu ke nan da faruwarsa, inda mutum 22 suka rasa rayukansu.
Galibin jam'iyyun siyasa a ƙasar sun dakatar da yaƙin neman zaɓe, sai dai fira ministar ƙasar ta ce za a ci gaba da yaƙin neman zaɓe ranar Litinin kuma za a gudanar da babban zaɓen ƙasar ranar Alhamis kamar yadda aka tsara.
Wani da ya shaida al'amarin ya ce ya ga lokacin da farar motar take tafiya cikin tsananin gudu a kan gadar Landan, gabanin ta fara bi ta kan mutane.
Ya ce akwai 'yan sanda hudu da suka ji raunuka (biyu daga cikinsu munanan raunuka), yayin da suke kokarin tsayar da motar.
An kashe maharan uku ne bayan mintuna takwas da kiran lambar gaggawa ta 999.
Wakilin BBC Holly Jones wanda yake kan gadar lokacin da lamarin ya faru ya ce motar "tana tafiya ne a guje kimanin Mil 50 a sa'a ɗaya" kuma ta buge "mutane shida ko biyar".
An yi Allah-wadai da harin
Shugaban Faransa Emmanuel Macro ya yi Allah-wadai da harin ranar Asabar.
Kuma akwai 'yan kasar Faransa huɗu da suka ji raunuka sanadiyyar harin.
Mista Macron ya yi waya da Fara Ministar Birtaniya Theresa May kuma ya ce Faransa "tana tare da Birtaniya fiye da kowane lokaci a baya".
Hakazalika, Fira Ministan Australia Malcolm Turnbull ya ce "yana sanya Birtaniya a addu'a" kuma ya ce mutum biyu daga kasarsa ne harin ya shafa.
Ɗaya yana asibiti, yayin da hukumomi suke kokarin gano halin da ɗayan yake ciki, kamar yadda Mista Turnbull ya shida wa manema labarai. Visit www.bestarewa.com.ng. for more news
No comments:
Post a Comment