Jami'an tsaro a kasar Saudiyya sun kama wasu 'yan Najeriya uku bisa zargin shiga kasar da miyagun kwayoyi, a lokacin da suka je aikin Umarah.
Rahotanni sun ce an cafke mutanen ne jim kadan bayan isarsu birni mai tsarki na Madinah.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya Abdullahi Mukhtar ya shaida wa BBC cewa duka mutanen da aka kama manyan mutane.
Ya kara da cewa suna zargin an shammace su ne aka sanya musu kwayar a kayansu, saboda yadda galibin manyan mutane a Najeriya ba sa son daukar kayansu da kansu yayin tafiya.
"Mutanen manya ne wadanda ba za a yi tunanin hannunsu a irin wannan aiki ba," in ji shi.
Sai dai kawo zuwa yanzu hukumar ba ta bayyana sunaye ko kuma jihohin da wadannan mutane suka fito ba.
Miliyoyin mutane ne suke isa kasar ta Saudiyya domin yin aikin Umarah a lokacin watan azumin Ramadan.
A baya dai an sha kama 'yan Najeriya a Saudiyya da kuma wasu kasashen duniya game da zargin aikata laifuka masu alaka da safara miyagun kwayoyi
Friday, June 2, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment