Follow Us @soratemplates

Sunday, June 11, 2017

Labari da dumi duminsa

An saki Saif al-Islam, ɗa na biyu ga marigayi shugaban Libya Kanar Muammar Gaddafi daga gidan kurkuku bayan an yi masa afuwa.
Saif al-Islam, wanda a baya aka yi zaton shi zai gaji mahaifinsa, ya shafe kusan shekara shida a hannun masu tayar da kayar baya a garin Zintan.
Kungiyar masu tayar da kayar bayan ce ta sanar ranar Asabar cewa ta sake shi.
A 2015 ne wata kotun da ke birnin Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa amma kungiyar ta ki amincewa ta mika shi.
A baya an bayar da rahoton karya cewa an sake shi.
Ina bindigar Muammar Gaddafi ta zinare?
"Rashin Saddam da Gaddafi masifa ce"
Kotun hukunta masu aikta manyan laifuka ta duniya, ICC tana nemansa ruwa-a-jallo domin yi masa shari'a kan zargin aikata laifuka take hakkin dan adam lokacin da mahaifinsa ya yi yunkurin murkushe 'yan adawa.
An kama Saif al-Islam, mai shekara 44, a watan Nuwamba na 2011 bayan ya kwashe wata uku yana buya sakamakon tumbuke gwamnatin mahaifinsa.
A baya ya taka muhimmiyar rawa wurin gina kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin mahaifinsa da kasashen yammacin duniya, kuma ana kallonsa a matsayin mai son kawo sauyi a gwamnatin.
Sai dai bayan an yi juyin-juya-halin 2011, an zarge shi da rura wutar rikici da kuma kashe masu zanga-zanga.
Har yanzu dai babu wata majiya daga gwamnatin kasar da ke Tripoli da ta tabbatar da sakin nasa, ko kuma kan wacce yarjejeniya aka sake shi.
Muhimman bayanai kan Saif al-Islam
Yunin 1972: An haife shi a birnin Tripoli, Libya, kuma shi ne ɗa na biyu ga Kanar Muammar Gaddafi
Fabrairun 2011: An soma tarzomar adawa da gwamnatin Gaddafi
Yunin 2011: Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya ta bayar da umarnin kama Saif al-Islam kan aikata laifukan take hakkin dan adam
Agustan 2011: Ya tsere daga Tripoli bayan 'yan tawaye sun kwace birnin; ya gudu zuwa Bani Walid
Oktoban 2011: An kashe mahaifi da kanensa
19 ga watan Nuwamba na 2011: Masu tayar da kayar baya sun kama shi a lokacin da yake kokarin shiga Jamhuriyar Nijar. An daure shi a Zintan
Yulin 2015: Kotun Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa ba tare da yana kotun ba
Yunin 2017: An bayar da rahoton sakinsa bayan an yi masa afuwa

No comments:

Post a Comment