Follow Us @soratemplates

Friday, June 9, 2017

Labari da dumi duminsa

Firai Ministar Birtaniya Theresa May tana fuskantar matsin lamba na ta yi murabus bayan da ta rasa samun rinjayen da take bukata don kafa gwamnati bayan samun sakamakon da yawa daga cikin kujerun majalisar dokokin Birtaniya.
Cikin masu kira da ta yi murabus har da jagoran jam'iyyar adawar kasar Jeremy Corbyn.
Sai dai farai ministar ta yi biris da kiraye-kirayen kuma ba ta nuna alamun za ta yi murabus.
Jam'iyyar da ta samu kujerun majalisar dokoki 326 cikin 650 da ake da su a kasar, ne za ta kafa gwamnati.
Ana ganin Jam'iyyar Conservative mai mulki tana kan gaba, amma kuma da wuya ta samu rinjayen da ake bukata da zai ba ta damar kafa gwamnati.
Babu jam'iyyar da za ta iya samun adadin kujerun da ake bukata. Don haka jam'iyyar da ta samu mafi rinjayen kujeru a zaben za ta kulla hadaka da karamar jam'iyya don su kafa gwamnati tare.
Sai dai ga alama wannan sakamakon ba zai yi wa Misis May dadi ba, saboda yadda ita ce bisa radin kanta ta kira zaben na ba zata a tunanin za ta samu gagarumin rinjaye, amma sai gashi reshe yana so ya juye da mujiya.
Nick Clegg ya faɗi a mazaɓarsa
Tsohon Mataimakin Farai Ministan Birtaniya Nick Clegg ya sha kayi a hannun dan jam'iyyar Labour a mazabar Sheffied Hallam.
Alex Salmond ya faɗi a mazaɓarsa
Hakazalika, tsohon Shugaban jam'iyyar Scotish National Party Alex Salmond ya sha kayi a mazabarsa ta Gordon.
Jim kadan bayan fara bayyana hasashen sakamakon zaben ne, darajar kudin kasar wato fam ya fadi idan aka kwatantashi da na dalar Amurka.
A watan Afrilu ne Farayi Ministar Birtaniya,Theresa May ta ba da sanarwar kiran zaben ba zata.
Misis May ta ce Birtaniya na bukatar yanayi na tabbas da zaman lafiya da shugabanci mai dorewa bayan zaben raba gardamar ficewa daga Tarayyar Turai da aka yi a bara.For visit www.bestarewa.com.ng

No comments:

Post a Comment