na yin wasu harkoki na kasuwanci ko na sana’a ba, sai dai kawai mace ta ce ita ’yar fim ce. To, amma a yanzu yanayi ya canja, ta yadda za ka ga da damansu a yanzu kowacce ta na yin harkokin kasuwancinta.
SAPNA ALIYU MARU na daya daga cikin jaruman fim mata da a yanzu su ke sahun manyan ’yan kasuwa, da ta ke shige da fice a cikin kasashe domin saye da sayarwa. Baya da kantin da ta bude a Dantsoho Plaza da ke titin Abdullahi Bayero a Kano.
WAKILIN LEADERSHIP A YAU ya tattauna da jarumar a game da yadda take gudana da kasuwancinta a matsayinta na jarumar finafinan Hausa. Shin ta daina aikin ne ko kuma tudu biyu take ci? Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasnace.
Sapna, sunanki ba boyayye ba ne a masana’antar finafinai ta Kannywood, amma dai za a iya cewa sama da shekara daya kenan an rabu da ganin ki. Wannan ya sa a ke ganin kamar kin bar harkar fim ne.
“Eh, haka ne, amma dai ni abin da zan fada Sapna dai ba ta daina yin fim ba, don fim sana’ata ce, babu yadda za a yi na daina, sai dai idan na yi aure kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi. Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shafi harkar kasuwanci wanda a yanzu su na saka a gaba. Kuma a yanzu ma fim na daina fitowa a ciki ban daina furodusin ba, kawai dai ba na fitowa ne a ciki.”
Kamar wanne irin kasuwanci ki ke yi?
“To, kasuwanci na yanzu ka ga a kantina ka zo ka same ina sayar da kayayyaki irin su atamfofi, leshi, takalma, agogo da ‘yan kunnaye da jakunkuna. To kuma wannan harkar ta sa ina da karancin lokacin da zan rinka zuwa lokeshin, saboda shi fim yana bukatar cikakken lokaci to ni kuma a yanzu ba ni da shi. Don haka idan na karbi aikin mutane ban san yadda zan yi a shi ba. Saboda kula da kanti da kuma zuwa na kawo kaya. Amma dai nan gaba kadan idan na gama saita harkokina masoyana za su ci gaba da ganina a fim.”
A yanzu kin kai tsawon wanne lokaci ba ki fito a fim ba?
“To, ina ganin dai a yanzu na fi shekara don tun fim dina mai suna Watarana, da muka yi fim din da Adamu a Kaduna, ina ganin tun daga ban kara fitowa ba.”
A matsayinki na jaruma, furoodusa, ko ya ya kike kallon harkar fim a wannan lokacin?
“To, gaskiya ana samun cigaba sosai don na ga ana fita aikin fim a koda yaushe don haka ci gaba ake samu da ko a baya aka samu ba za a samu haka ba, don haka an samu ci gaba ta kasuwa da kuma kayan aiki, ni dai a yadda nake gani kenan.”
Me ya sa a yanzu ba a samun jarumai masu yawa da ake yayi, kamar da sai ki ga mata da yawa ana yayinsu amma a yanzu sai dai daya ko biyu?
“To, abin da ya sa yanzu idan ka duba a ba cika tsayawa ba a fim kadai kusan kowacce jaruma tana da harkokinta na kasuwanci da take yi don haka yanzu an daina tsayawa ana jiran a yi fim sai ake hadawa da kasuwanci. To irin wannan sai ka ga wata ma idan ana neman ta ta fito a fim sai ka ga ba ta a lokaci kamar a baya don haka za ka ga duk an ragu wasu kuma sun yi aure ba a samu wadanda suka maye gurbin su ba. ”
Amma ba kya ganin a matsayinki na ‘yar kasuwa nan gaba idan kika dawo za ki yi fim sai a ga kudin da za a ba ki sai furodusa ya shirya don kada ki raina?
“Ai ba haka ba ne shi dan fim duk wata alfarma da ya samu a duniya ta hanyar fim ce, don haka duk ina ya je ya dawo fim ne gatansa, don haka ko nawa za a bai wa mutum ba zai raina ba. Don tun kadin ya zama wani abu ya san haka ake biyan a don haka ba wani abu ne daban ba.”
To, ya ya kike iya gudanar da kasuwancinki a matsayinki na jaruma da kowa ya san fuskarki?
“Ina jin dadi sosai don ka ga su ‘yan fim suna da alfarma. Sau da yawa idan na je waje ko da ana hana mutane shiga sai ka ga an bar ni na shiga. Aga an ga ni ‘yar fim ce. Don haka ina jin dadin sosai kuma wasu ma saboda sun san kai dan fim ne suna zuwa sayan kaya wajena. Don su zo su ganni kuma duk fim ne ya ja min wannan alfarma.”
To ya ya mu;malar ki take a yanzu da ‘yan fim?
“Mu’amala ta tana nan kamar dai muna tare da su kamar tare muke kuma na fada maka ina furodusin don haka koyaushe muna tare sai dai idan na tafi wajen kasuwancina.”
Daga karshe wace shawara kike da ita musamman ga mata ‘yan fim?
“To, shawarata a garesu ita ce, lokaci ya yi da za su gane harkar fim kadai ba za ta rike su ba. Domin kuwa suna cikin fim din za su yi aure. Kuma idan sun yi aure ba za su ci gaba da fim ba, don haka su raba kafa su rinka hadawa da kasuwanci ta yadda ko da sun yi aure za su ci gaba da yin kasuwancinsu.”
To, madalla mun gode.
“Ni ma na gode.”
-LEADERSHIP
Wednesday, April 25, 2018
Kannywood : Babu Yadda Za’a Yi In Daina Sana’ar Fim – Sapna Aliyu
by
Bestarewa
on
April 25, 2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment