Kodayake Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 ba, amma na kusa da shi sun sha bayyana cewa babu abin da zai hana shi yin tazarce.
A watan Mayun shekarar 2015 ne Shugaba Buhari ya yi rantsuwar fara mulkin wa'adin shekara hudu karkashin jam'iyyar APC, kuma yana da damar sake neman wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.
Sai dai akwai wadanda suke ganin bai kamata shugaban ya nemi tazarce ba, ciki har da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Mun yi nazari kan mutanen da ake ganin za su iya kawar da Shugaba Muhammadu Buhari daga kan mulki a zabe mai zuwa?
Sanata Bukola Saraki
Mutum na biyu cikin manyan 'yan siyasar kasar wanda ake ganin watakila ya nemi tsayawa takarar shugabancin Najeriya shi ne Shugaban Majalisar Wakilai Sanata Bukola Saraki.
Kodayake a halin yanzu ya musanta hakan, amma a baya sau biyu yana neman tsayawa takarar shugabancin kasar.
Sai dai wadansu suna ganin da wuya Sanata Saraki ya iya samun tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyarsa ta APC, musamman ma idan Shugaba Buhari zai yi takara.
Amma dai yana da alaka da 'yan siyasa, ga kudi, ga kuma kwarewa a siyasance.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Har ila yau, a zauren majalisar dattawan kasar, akwai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ma ya taba neman shugabancin kasar a 2015 amma Buhari ya kayar da shi a zaben cikin gida a APC.
Kodayake a wannan karon bai bayyana aniyyarsa ba tukunna, amma alamu na nuna cewa har yanzu bai hakura ba, kuma watakila ya kara gwada sa'arsa.
Tsohon gwamnan jihar Kanon shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na 'yan takarara neman shugabancin a jam'iyyar APC a zaben 2015.
Masana suna ganin a wannan karon, zai iya samun tikitin shugabancin kasa a jam'iyyar musamman idan Shugaba Buhari ya ki amincewa ya sake yin takara.
Alhaji Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yana daya daga cikin mutanen da ake ganin za su sake gwada sa'arsu, bayan ya nemi zama shugaban kasar har sau uku a baya.
Akwai wadanda suke ganin sha'awarsa ta zama shugaban Najeriya ce ta sa ya koma jam'iyyar PDP daga jam'iyyar APC mai mulki a watan Disambar bara.
Ga dukkan alamu Alhaji Atiku Abubakar yana ganin zai fi samu damar kara gwada sa'arsa a jam'iyyar PDP.
Sai dai wasu na ganin ba lallai ne jam'iyyar ta ba shi tikitinta ba.
Ayodele Fayose
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose shi ne wanda ya fara bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP.
Gwamnan Fayose wanda an riga an fara yada hotunan kamfe dinsa a fadin kasar, mutum ne da ke yawan nuna adawarsa ga jam'iyyar APC da kuma Shugaba Buhari.
Gwamnoni suna da matukar tasiri a siyasar Najeriya, abin da ya sa wadansu masana suke ganin kila shi ya sa Mista Fayose yake kokarin ganin ya gwada sa'arsa.
Alhaji Sule Lamido
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa yana daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya da ake ganin watakila shi ma ya nemi takarar shugabancin kasar a zaben 2019.
Sai dai shi ma bai fito fili ya bayyana aniyyarsa ta yin hakan ba tukunna.
Alhaji Sule Lamido yana daya daga cikin wadanda suke sukar gwamnatin APC da Shugaba Buhari.
Shin 'yan majalisa na shirin yi wa Buhari wayo a zaben 2019 ne?
Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 - Malami
2019: Ministar Buhari 'ta fara yi wa Atiku kamfe'
Malam Jafar Jafar wani mai sharhi ne kan harkokin siyasar Najeriya, kuma ya ce yana ganin duk wani dan siyasa da yake neman takara a jam'iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne kawai, "matukar Shugaba Buhari zai sake yin takara."
Ya ce: "Idan har Buhari zai yi takara, to babu makawa jam'iyyarsa shi za ta tsayar a zaben 2019."
"Kuma da wahala a ce ba zai yi takara ba," in ji shi.
Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu muradin yin takara a jam'iyyar APC shi ne kawai su sauya jam'iyya.
"Ga jam'iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta iya faduwa zabe."
"Saboda a gaskiya farin jinin jam'iyyar da na Shugaba Buhari ya ragu sosai."
Mai fashin bakin ya ce abin da ya sa manyan 'yan siyasar kasar ba su fito sun bayyana aniyarsu ta takara ba, "shi ne kamar wata dabara ce suke don su fito tashi guda idan lokacin fara yakin neman zabe ya yi."
'Yan kasar dai sun zuba ido su ga jerin mutanen da za su fito su bayyana aniyarsu ta neman kuri'unsu
Wednesday, April 25, 2018
Siyasa Nigeria : Su waye za su ja da Buhari a zaben 2019?
by
Bestarewa
on
April 25, 2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment