Shugaba Osinbajo na nade-naden guraben da Buhari bayyi ba
- Ana ganin kamar yana saka nasa yaran ne
- An gano wasu masu kashi a jika kuma a hukumar kamo beraye
A sabbin nade-nade da shugaba Osinbajo keyi gabanin dawowar shugaba Buhari, a makon jiya ne ya nada 'yan kwamitin da zasu tafiyar da hukumar ICPC mai sa ido kan masu tu'annati da kudin kasa.
Sai dai cikin mambobin guda goma sha hudu, biyu daga cikinsu an taba bincikarsu kan wata badakala ta biliyoyin Nairori. Wadannan sune Maimuna Aliyu da ma Sa'ad Alanamu.
Katobara! Sabbin nade-naden shugaba Osinbajo wai harda 'beraye'
A ruwaitowar ICIR, wadannan mutane ana bincikarsu kan manyan badakaloli ta dumbin kudade, Alanamu a jiharsa ta Kwara a waccan gwamnatin, ita kuwa Maimuna, a cewar rahoton, tayi kaurin suna wajen waskewa da dukiyar gwamnati.
A cewar majiyar ta bestarewa.COM.ng
dai, hukumar ta ICPC na cikin shirin mika sunan Maimunatu a kotu ne, kwatsam sai hukumar ta ji ma ai wai ashe an nada ta shugabancin hukumar a
A cikin rahoton ICIR din dai, baya ga haka, a baya ma ana zargin ta da almundahana da dukiyar jama'a a bankin Aso Savings Ltd, a Abuja, lokacin tana shugabantar sa. Kuma ma EFCC ce da hukumar 'yan-sanda a kan kes din.
Badakalar dai ta hada da gidaje da filaye wadanda wai ta siyar ba bisa ka'ida ba.
Wannan a iya cewa anyi nadin auren gwauro amma tuzuru ya biyo tawagar kenan.
Saturday, August 5, 2017
Labari da dumi duminsa daga fadar shugaban kasan Nigeria
by
Bestarewa
on
August 05, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment