- Sanata Kwankwaso ya kauracewa taron jamâiyyar mai mulki ta APC shiyar jihar Kano
- Ana sa ran za a yi zaben sabbin kwamitin zartarwa na jam'iyyar a taron
- An gabatar da mutane 15 ba tare da wata hamayya ba don cika gurbin ofisoshi 15 na jamâiyyar
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kauracewa taron jamâiyyar mai mulki ta APC shiyar Kano wanda ake gudanar a halin yanzu a Kano.
Taron, wanda ake gudanar a cikin zauren filin wasa na Sani Abacha, ta samu halartar gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje da âyan majalisar jihohi da na tarayya da wasu jigon âyan siyasa da kuma shugabannin jam'iyyar don zaben sabbin kwamitin zartarwa na jam'iyyar a jihar.
Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Kwankwaso, wanda yake yanzu sanata, ya kasance a kafar wando da gwamna Ganduje a kan jagorancin jamâiyyar APC a jihar Kano. Ganduje shi ne mataimakin gwamnan ga Kwankwaso har karshen watan Mayu 2015 lokacin da ya bar ofis a matsayin gwamna jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso
A zaman taron jamâiyyar a jihar, mutane 15 masu biyayya ga gwamna Ganduje aka gabatar ba tare da wata hamayya ba don cika gurbin wasu matsayi 15 a kwamitin sashen zartarwa na jama'iyyar.
Mutanen sun hada mukaddashin shugaban jam'iyyar na yanzu, Abdullahi Abbas a matsayin anihin shugaban jamâiyyar. mataimakinsa, Shehu Maigari da kuma sakataren jamâiyyar na yanzu, Ibrahim Sarina.
Saturday, August 5, 2017
Wai shin Mai yahana senata Dr Rabi.u Musa kwankwaso rashin zuwa Taron APC na jahar Kano !!!
by
Bestarewa
on
August 05, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment