Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru, ya yi watsi da ji-ta-ji-tar da ake bazawa cewa wai Sanata Kwankwaso ne ya tsayar a matsayin gwanin sa a zaben shugaban kasa a 2019.
Wannan ji-ta-ji-ta dai ta biyo bayan bude ofishin kamfen na Kwankwaso da aka yi a Dutse, babban birnin jihar Jigawa a makon da ya gabata. An dai ce wasu makusantan Badaru sun halarci bikin.
Sai dai kuma yayin da ya ke maida raddi ta hannun kakakin sa, Bello Zaki, Gwamna Badaru ya ce maganganun da ake bazawa cewa Badaru ya saki akalar Shugaba Buhari ya kama akalar Kwankwaso, duk shirme ne kuma ba su da tushe.
Zaki ya ce taron bude ofishin kamfen na Kwankwaso a Dutse, ba shi da bambanci da sauran tarukan kowace jam’iyya, wanda gwamnatin jihar ba ta da ikon hanawa.
Taron dai makusancin Badaru ne ya shirya shi, wanda kuma shi ne Manajin Darakta na gidan talbijin na jihar Jigawa.
A wurin taron dai an bai wa Daraktan Malam Hadeja nauyin bude ofis, sannan kuma ya yayata kyawawan akidun Kwankwaso a dukkan kananan hukumomin Jigawa 27.
Sai dai kuma duk da hakan, Zaki ya ce kasancewar Hadeja a wurin taron ba shi da wata dangantaka da Gwamna Badaru.
‘‘Don mutum na mukarrabin Gwamna Badaru, hakan ba ya na nufin ba ya da wani abin yi na kashin kan sa ba, sai abin da Badaru kawai ya ke so shi zai yi.” Inji Zaki.
Tuesday, July 25, 2017
Bance kwankwasone gwani na ba azaben komai yasa haka?
by
Bestarewa
on
July 25, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment