Shugaban hukumar EFCC yace ba sani ba sabo a yaki da almundahana
- Magu ya bayyana haka ne a ranar da suka gudanar da tattaki a Abuja
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da almundahana da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa babu wani shafaffu da mai a yakin da suke yi da almundahana, inji rahoton Daily Trust.
Magu ya bayyana haka ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu yayin da hukumar take gudanar da tattakin yaki da cin hanci da rashawa a garin Abuja, inda ya bayyana cewa ba sani ba sabo a yakin da suke yi.
KU KARANTA: Bashin gaba: yan ƙabilar Tiv da Jukun sun kashe junansu sakamakon rikicin ƙabilanci
“Hukumar EFCC ta nuna cewa babu wani shafaffe da mai a yaki da rashawar da muke yi, duk girmanka duk matsayinka, sai mun kama mutum. Don haka ne ya sa wasu masu uwa a gindin murhu ke ganin sai sun lalata mana kokarin da muke yi.” Inji Magu.
Bestarewa.com.ng
Ibrahim Magu
“Mutanen nan basu da mutunci, kuma suna yin duk abinda zasu iya yi don yakar mu, suna son mayar damu zamanin sata da almundahana.” Inji shi.
Daga karshe Magu ya gode ma yan Najeriya dake basu goyon baya, inda yace da dama daga cikin yan Najeriya na son a zafafa hukunci akan barayin gwamnati, kamar yadda majiyar bestarewa.com.ng ta ruwaito.
Sa’annan ya gargadi dukkanin manyan mutane dake da kashi a gindinsu dasu kuka da kansu, don kuwa ba zai sassuata musu a yakin da yake yi da almundahan da rashawa ba, “ da ikon Allah zamu samu nasara, kuma rashawa yak au a Najeriya har abada.”
Saturday, July 15, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment