Follow Us @soratemplates

Monday, September 25, 2017

Hausa News:- Zamu Fara Ta Yankin Maiduguri Inji Morell Da Classiq (Shiga Kaga Me Zasu Fara

Abin Kamar Da wuya Yadda Morell Da Classiq Zasu Mai Da Mai Duguri Cikin Farin Ciki, Yayin Da sojoji ke neman kawo karshen wannan kungiyar yan ta’adda daga kasar, matasan Maiduguri inda kungiyar ta samu asali sun koma ga waka domin samun annashuwa daga barnar da yan ta’addar suka yi a garin
, Shima Fitaccen mawaki Morell Dan jihar Borno ne, Sai Kuma Classiq Dan Jahar Bauchi Ne

A Maiduguri babban birnin jihar Borno dake yankin Arewa maso gabashin Nijeriya ta soma komawa kamar yadda take wajen samun nishadi domin matasan garin sun koma ga harkar waka kuma wuraren nishadi sun fara koma yadda suke a da.

Yayin da wasu ke ganin cewa jihar Borno ya koma tamkar kamar filin yaki tsakani yan boko haram da sojoji, wasu matasan jihar suna son su sauya tunanin mu inda suke nuna halin walakin goro a miya game da harkar zamantakewa da nishadi dake faruwa a jihar.

Boko haram ta fara ta’addancin ta a wannan jihar kuma sunyi sanadiyar rasuwar sama da mutane 20,000 tare asarar dukiyoyi fiye da kimani har ma da sa wasu da dama yin balaguro zuwa wata jiha har ma da kasashen waje.

Ganin cewa sojin sun fara samun nasara wajen korar wannan kasurgumin kungiyar ta’addanci da ta addabi al’ummar jihar matasan garin sun koma ga waka domin nishadantar da junansu don kawar da matsaloli da yan ta’adda suka haifar a zukatan al’ummar jihar.

Sannu bata hana kaiwa da haka matasa suka daura domin faranta ma kansu rai inda suka koma ga nishaÉ—i domin kawar da barnar da rikicin boko haram ya haifar a jihar su.

Marubucin jaridar GuardianEromo Egbejuleya ruwaito cewa gidajen shakatawa na dare watau ‘club’ sun cigaba da tafiyar da alamuran su a cikin garin ba tare da fargaba.

Cikin ayyukan da matasan keyi yanzu akwai hada fagen yin wakar domin fitar da basirar su ga idon jama’a.

Mazaunan garin sun samun annashuwa bayan tserewar kungiyar domin neman tsira.

Yanzu kungiyar kwallon kafa ta jihar watauEl-kenemi warriorssun koma da taka-leda a jihar kuma daliban jami’arMaidugurisun koma sahun da suka kafa na shirya wasanni don moriyar junansu.

A kwanan baya daliban makarantar sun shirya bikin kammala karatu wadda har ma suka gayyato fitattun mawakan yankin arewaClassiq da Morell

Domin Ganin Yadda Wannan Wassannin Nasu Zasu Gudana A Yankin Jahar Borno, Sai Ku Kasance Tare Damu A Koda Yaushe.

No comments:

Post a Comment