Follow Us @soratemplates

Friday, September 22, 2017

Video: Ku Kalli Hadiza Gabon Itama Ta Fito A Film Din Nollywood

Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Fitacciyar jarumar nan ta finafinan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a finafinan Nollywood da ake yi a kudancin Nijeriya.
Jarumar ta shaida wa BBC Hausa cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin finafinai a bangarori daban-daban.
A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.
“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.
Hadiza Gabon ta kara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al’adata ba”.
Jarumar ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a Fina Finan Nollywood.



DOWNLOAD VIDEO HERE

No comments:

Post a Comment