Addu’a yayin kiran Sallah :
Wanda ya ji kiran sallah zai fadi dukkan abin da ladanin yake fadi, sai dai idan yace;
ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟﺼَّﻼَﺓِ، ﺣَﻲَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻔَﻼَﺡِ .
Hayya Alas Salah, Hayya Alal Falah.
Ku taho ga Sallah, ku taho ga babban rabo.
Maimakon haka sai shi ya ce:
ﻻ ﺣَـﻮْﻝَ ﻭَﻻ ﻗُـﻮَّﺓَ ﺇِﻻّ ﺑِﺎﻟﻠﻪ .
La hawla wala kuwwata illa billah.
Babu daraba, babu karfi sai da Allah.
ﻭَﺃَﻧﺎ ﺃَﺷْـﻬَﺪُ ﺃَﻥْ ﻻَ ﺇِﻟَـﻪَ ﺇِﻻّ ﺍﻟﻠﻪُ ﻭَﺣْـﺪَﻩُ ﻻَ ﺷَـﺮﻳﻚَ ﻟَـﻪُ، ﻭَﺃَﻥَّ ﻣﺤَﻤّـﺪﺍً ﻋَﺒْـﺪُﻩُ ﻭَﺭَﺳُـﻮﻟُﻪُ ، ﺭَﺿِﻴـﺖُ ﺑِﺎﻟﻠﻪِ ﺭَﺑَّﺎً ، ﻭَﺑِﻤُﺤَﻤَّـﺪٍ ﺭَﺳُـﻮﻻً ﻭَﺑِﺎﻹِﺳْﻼﻡِ ﺩِﻳﻨًﺎ .
Wa-ana ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-anna Muhammadan AAabduhu warasooluh, radeetu billahi rabban wabimuhammadin rasoolan wabil-islami deena.
Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini.
Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sannan ya ce:
ﺍﻟﻠّﻬُـﻢَّ ﺭَﺏَّ ﻫَﺬِﻩِ ﺍﻟﺪّﻋْـﻮَﺓِ ﺍﻟﺘّـﺎﻣَّﺔِ ﻭَﺍﻟﺼّﻼﺓِ ﺍﻟﻘَـﺎﺋِﻤَﺔ ﺁﺕِ ﻣﺤَـﻤَّﺪﺍً ﺍﻟﻮَﺳﻴـﻠﺔَ ﻭَﺍﻟْﻔَﻀـﻴﻠَﺔ ﻭَﺍﺑْﻌَـﺜْﻪُ ﻣَﻘـﺎﻣًـﺎ ﻣَﺤْـﻤُﻮﺩﺍً ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻭَﻋَـﺪْﺗَﻪُ ﺇِﻧَّـﻚَ ﻻ ﺗُـﺨْﻠِﻒُ ﺍﻟْﻤِﻴـﻌَﺎﺩَ .
Allahumma rabba hathihid-da'watit-tammah, wassalatil-ka-imah ati Muhammadan alwaseelata wal-fadeelah, waba'ath-hu makaman mahmoodan allazee wa'adtahu, innaka la tukhliful-mee'ad.
Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.
Sannan ya yiwa kansa addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu'a a wannan lokaci ba a kin karbarta
Wednesday, May 31, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment