WASU NASSOSHI DAGA QUR'ANI DA SUNNAH AKAN FALALAR AZUMI:
1- قال الله تعالى: (شهر رمضان الذي أنزل فيه القرآن) الآية[سورة البقرة].
Allaah madaukakin Sarki Yana cewa: (Watan Ramãdan wanda a cikin Sa aka saukar da Al -QUR'ÃNI).
2- عن أبي أمامة رضي الله عنه أنه قال: يا رسول الله، مرني بأمر ينفعني الله به، قال: (عليك بالصوم فإنه لا مثل له) رواه النسائي وهو حديث ثابت.
Daga Abu-Umãmatal Bãhiliy (r.a) yace: Ya Manzon Allaah ka umurceni da wani al'amari wanda Allaah zai amfaneni wurin Allaah, Sai Manzon Allaah(saw) Yace: (Ka lizimci azumi, saboda babu irinshi).
3- عن سهل بن سعد رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وآله وسلم قال: (إن في الجنة بابا يقال له الريَّان، يدخل منه الصائمون يوم القيامة، لا يدخل منه أحد غيرهم، يقال: أين الصائمون؟ فيقومون، لا يدخل منه أحد غيرهم، فإذا دخلوا أغلق، فلم يدخل منه أحد) متفق عليه.
Daga Sahl bn Sa'ad (r.a) Lallai Annabi (saw) Yace: (A Aljannah akwai kofa da ake kiran shi AR-RAYYÃN, masu azumi zasu shiga ta cikin shi ranar Al- Qiyãmah, babu wanda zai shiga ta kofar sai su. Za'a ce ina masu azumi? Sai su mi'ke, babu wadanda zasu shiga ta wannan kofar sai su, idan suka shiga sai a kulle, saboda haka babu wanda zai sake shiga bayan su).
4- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (يا معشر الشباب! من استطاع منكم الباءة فليتزوج، فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج، ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Yaku matasa! Wanda yake da hali yayi aure, saboda shi yafi kame ido (gani) dakuma kiyaye farji, wanda kuma bashida halin aure to yayi azumi; domin azumi kamar dandaqa ne (yana rage sha'awa).
5- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (الصوم جُنَّة يَستجن بها العبد من النار) رواه أحمد وهو ثابت أيضا.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi garkuwa ne da bawa ke kare kanshi daga shiga wuta).
6- عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: (قال الله تعالى: كل عمل ابن آدم له إلا الصيام، فإنه لي وأنا أجزي به )، وفي رواية لمسلم: (كل عمل ابن آدم يضاعف، الحسنة بعشر أمثالها إلى سبعمائة ضعف، قال الله عز وجل: إلا الصوم، فإنه لي وأنا أجزي به، يدع شهوته وطعامه من أجلي) متفق عليه.
Daga Abū Harairah (r.a) yace: Manzon Allaah (saw) Yace: (Allaah SWT Yace: Kowane aiki na dan adam ne banda azumi, domin azumi nawa ne kuma NI zan bada sakamakon shi), A riwayar Muslim kuwa Yace: (Ana ninka kowane aiki na dan adam, kowane lada za'a ninka shi sau goma har zuwa ninki ďari bakwai, sai Allaah Yace: sai azumi, domin shi nawa ne kuma NI ne zanyi sakayya akansa, dan adam yakan bar sha'awar shi da abincin shi da saboda NI).
7- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (الصيام والقرآن يشفعان للعبد يوم القيامة، يقول الصيام: أي رب منعته الطعام والشهوات بالنهار فشفعني فيه، ويقول القرآن: منعته النوم بالليل فشفعني فيه، قال: فيُشَفَّعان). رواه أحمد وهو حديث ثابت.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Azumi da Al - Qura'ni zasu ceci bawa ranar Al-Qiyãmah, azumi zaice: Ya Ubangiji na hanashi abinci da abubuwan sha'awa da rana Kabani ceton shi, shi kuma Qur'ani zaice: Na hanashi bacci da dare dan haka kabani ceton shi, sai Manzon Allaah Yace: Sai abasu ceton su).
8- قال رسول الله صلى عليه وآله وسلم: (من صام يومًا في سبيل الله باعد الله وجهه عن النار سبعين خريفا) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Duk wanda ya azumci rana ďaya dan Allaah, Allaah Zai nisantar da fuskar shi daga wuta tsawon shekaru saba'in).
9- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (للصائم فرحتان: فرحة عند فطره، وفرحة عند لقاء ربه، ولخلوف فم الصائم أطيب عند للله من ريح المسك) متفق عليه.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Mai azumi yanada farin ciki biyu: Farin ciki sanda zaiyi buďa baki, da Farin ciki lokacin haďuwa da Ubangijin shi, Tabbas! Bashi (wari) na bakin mai azumi yafi 'kanshin almiski kyawu da daďi a wurin Allaah).
10- قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (فتنة الرجل في أهله، وماله، وجاره تٌكِّفرها: الصلاة، والصيام والصدقة) رواه البخاري.
Manzon Allaah (saw) Yace: (Fitinar mutum a iyalinshi, da dukiyarshi, da ma'kwabcinshi; Sallaah da Azumi da Sadaqah suna kankare su).
11- عن زيد بن خالد الجهني رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم -: (من فطر صائمًا كان له مثل أجره غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيئًا) رواه الترمذي وابن ماجه وهو ثابت.
Daga Zayd bn Khalid Al-Juhaniy (r.a) Yace: (Duk wanda yacida mai azumi Allaah zaibashi kwatankwacin ladan shi batareda an rage ko kadan daga ladan mai azumin ba).
12- عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وآله وسلم قال: (ثلاثة لا تردُّ دعوتهم: الإمام العادل، والصائم حتى يفطر، ودعوة المظلوم) رواه الترمذي وابن ماجه وهو حديث ثابت أيضا.
Daga Abu Hurairah (r.a) Annabi (saw) Yace: (Mutane uku ba'a mayar da addu'ar su: Jagora adili, Mai azumi har zuwa buďa bakin sa, dakuma addu'ar wanda aka zalunta).
Allaah Ya amshi ibadojin mu.
Ďan'uwanku: A Y A
Saturday, May 27, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment