A Najeriya, yayin da ƙananan ma`aikata da sauran masu ƙaramin ƙarfi ke neman hanyar mallakar muhalli ido-rufe, wasu gidajen da gwamnati jihar Kano ta gina sun kama hanyar yin kwantai.
Har yanzu dai mutane ba su shiga rukunin gidajen Kwankwasiyya City da Amana City da kuma Bandirawo City ba, wadanda gwamnatin Engineer Rabiu Musa Kwankwaso ta gina.
Wani mai ƙaramin ƙarfi a jihar Haruna Ado Umar ya ce ya kan ji matukar taikaci idan ya ga gidajen babu kowa a ciki.
'Babu yadda za'a yi mai ƙaramin ƙarfi ya mallaki gida na miliyan 27', in ji shi.
Gwamnatin Ganduje dai ta ce ta gagara sayar da gidajen ne saboda masu ƙaramin ƙarfi na kukan cewa sun yi matukar tsada.
Ta kara da cewa tuni da dukufa wajen gina wasu sabbin gidaje masu daki uku-uku da ake sayar da su akan Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da hamsin wadanda masu ƙaramin ƙarfin zasu iya saye.
Sai dai wasu masana sun ce kamata ya yi a bada hayan gidajen da ba'a sayar ba kasancewar sun yi tsada ga masu son saye.
No comments:
Post a Comment