Follow Us @soratemplates

Saturday, May 27, 2017

LABARAN WASA

Za a rufe saman babban filin wasan kwallon kafa na Wales don yin wasan karshe na gasar Zakarun turai ta 2017 da za a yi a birnin Cardiff saboda dalilai na tsaro.
Sama da 'yan kallo 170,000 ne ake sa ran za su je birnin domin kallon karon-batta tsakanin manyan kungiyoyin Juventus da Real Madrid ranar uku ga watan Yuni.
Shi ne zai kasance wasan karshe na farko da aka buga cikin rufaffen filin wasa.
Hukumar kwallon kafa ta Wales dai ta ce tabbatar da tsaro shi ne "babban abin da ke gabanta".
An bayar da shawarar rufe saman filin wasan ne saboda fargabar kai hari da jirgi maras matuki a kan abin da aka bayyana da wasa mafi girma tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a duniya.
Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, hukumar ta ce ta dauki matakin rufe saman filin wasan bayan yin la'akari da "bukatar hakan daga hukumomi".
Za kuma a rufe saman filin wasan a lokacin da kungiyoyin za su yi atisaye a filin wasan ranar Juma'a biyu ga watan Yuni.

No comments:

Post a Comment