Abubuwa da dama sun faru tun bayan kafuwar fannin fina-finai na Kannywood fiye da shekara 20, sai dai akwai fitattun abubuwan da suka fi janyo cece-kuce musamman a 'yan shekarun baya-bayan nan.
Mun yi nazari kan abubuwa biyar da suka fi tayar da kura a a masana'antar, wacce ke da farin jini sosai:
1. Auren jinsi
Wani abu da ya jan hankali sosai kuma ya tayar da jijiyar wuya shi ne zargi hada auren jinsi da aka yi wa wasu taurarin Kannywood hudu da yi a birnin Kano a watan Afrilun shekarar 2007.
Lamarin da ya sa suka shiga buya, bayan hukumar shari'a ta Hizba ta samu labarin sannan ta shiga nemansu.
Ko da yake a wata hira da BBC Aunty Maiduguri wadda aka zarga da hada auren ta musanta zargin.
2. Fim din batsa ko Blue Film
'Yan Kannywood sun samu kansu a tsaka mai wuya a watan Agustan shekarar ta 2007, inda aka zargi Maryam Usman Hiyana da Saurayinta Usman Bobo da yin fim din batsa.
Fim din da aka yita yadawa kuma ya janyo matukar suka ga masu harkar fina-finan.
Fim din batsan ne kuma ya kawo karshen fitowar Hiyana a fina-finan Hausa bayan an kore ta.
3. Zargin luwadi
A watan Agustan bana ne kuma zargin luwadi ya dabaibayi masana'antar.
Lamarin da ya kai har fitaccen jarumin nan kuma mawaki, Adam A Zango, rantsuwa da alkur'ani mai tsarki yana kare kansa.
Batun ya taso ne bayan da aka zargi wasu daga cikin masu harkar fimdin da cewa 'yan luwadi ne.
Sai dai a wannan karon babu wani da aka fayyace sunansa.
4. Gina alkaryar fim
Batun gina alkaryar fim a jihar Kano wanda gwamnatin tarayyar ta so gudabarwa ya tayar da jijiyoyin wuya a baya a watan Julin bana.
Malaman addini da jama'a ne suka nuna adawa da shirin, suna masu cewa zai daurewa badala da shashanci gindi a jihar.
Sun zargi 'yan fim da cewa mutane marasa kamala da ke yada batsa.
Sai dai masu shirya fim din sun ce ba haka lamarin ya ke ba, kuma mummunar fahimta ake yi musu.
5. Rahama Sadau ta rungumi Classiq
Batun rungumar mawakin nan, Classiq da Rahama Sadau ta yi shi ne abu na baya-bayan nan da ke jan hankali masu bin al'amuran Kannywood da ma jama'ar gari.
Yayin da wasu ke sukarta kuma kungiyar shirya fina-finan Hausa ta kore ta, Rahama ta nemi gafara tare da kokarin fahimtar da mutane cewa duk abin da ta yi a wakar aikinta ne ya bukaci haka ba son rai ba.
Kungiyar ta ce 'yar wasan ta yi karan-tsaye ga ka'idojin kyawawan dabi'un da Kannywood ta ginu a kansu, lamarin da ta ce shugabannin harkar ba za su lamunce da shi ba.
Sai dai wasu na korafin cewa akwai wasu 'yan wasan da a cewarsu suka yi abin da ya fi na Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba.
Masu korafin na ganin an kawar da kai ga abin da taurarin fina-finai kamar su Ali Nuhu da Sani Danja da kuma Adam A Zango ke yi a wasu fina-finan ko wakoki.
Ko da yake wani jami'i ya shaida wa BBC cewa matakin da suka dauka kan Rahama wani bangare na yunkurin gyara al'amura a Kannywood, kuma nan gaba doka za ta hukunta duk wanda ya keta ta.
Saturday, July 8, 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment