An yi jana'izar mutum goma a Zamfara, dukkaninsu iyalan wani dan majalisar dokokin jihar, wadanda suka mutu a sanadiyyar hadarin mota.
Motar da suke ciki ce ta yi taho-mu-gama da wata babbar motar dakon kaya a ranar Lahadi, yayin da suke koma wa gida daga hidimar aure.
An dai yi jana'izar mamatan a garinsu na 'Yarkufoji dake karamar hukumar Bakura.
Wakilin BBC ya ce tafiya ce ta farin ciki da neman karuwa, to amma sai kwatsam ta rikide ta koma ta rashi da matukar jimani.
Iyalan dan majalisar mai wakiltar mazabar Bakura a majalisar dokokin jihar ta Zamfara, Hon Saidu Danbala 'Yarkufoji ne dai hadain motar ya rutsa da su.
Jami'in hulda da jama'a na Majalisar dokokin jihar Zamfara, Malam Nasiru Usman Beriki, ya ce hadarin ya faru ne bayan sun isa garin Gusau domin hidimar auren daya daga cikin 'yayan Hon Saidu.
"Bisa hanyarsu ta komawa gida ne bayan sun bar Gusau, sun wuce Bungudu, sun kai gadar da ke fita garin Bungudu, suka hadu da wata babbar mota wadda ta ke dauke da kwalaben lemu", in ji shi.
"A cikin mutum goma da suka rasu, akwai 'yayansa mata uku da dan shi namiji daya, da jikokinshi uku, da dangin matarsa su biyu, da kuma direban motar"
Malam Nasiru ya ce matarsa da kuma jaririnta sun tsira .
Hatsarin mota ya hallaka mutane 18
An haifi jariri shekaru 4 bayan mutuwar iyayensa
Jami'in wayar da kan jama'a na Hukumar Kiyaye Haduran ta Kasa FRSC reshen jihar ta Zamfara, Malam Nasiru Ahmad ya shaida wa BBC cewa baya ga iyalan dan majalisar jihar da suka rasu, yaron babbar motar da suka yi karo da ita, shi ma ya rasu.
Wannan hadari dai ya kara fito da irin yadda jama'a ke rasa rayukansu a haduran mota a kasar, galibi sanadiyyar rashin kyawun hanyoyin, da tukin ganganci da gudun fiye da kima.
Tuesday, April 24, 2018
Labaran duniya : Yadda dan majalisa ya rasa iyalansa 10 a rana daya
by
Bestarewa
on
April 24, 2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment