Follow Us @soratemplates

Monday, July 10, 2017

Kannywood labarai

Mawaki Ahmad M. Sadiq sananne mawaki ne, ajin farko da ya dade ana damawa da shi a duniyar finafinai ta Kannywood. Sai dai ba kowa bane ya san cewar mawaki kuma fitaccen mai hada kida yana da wakoki akalla 200 ko kasa da haka.
M. Sadiq, kamar yadda aka fi kiransa a Kannywood ya yi ta maza, ya zarce wane da wani ciki har da su yallabai, ya samo wata sarauniyar kyau zai kara akan wata sarauniyar kyau da ya ke da ita a gida.
Ko ba komai dai, ai ance biyu ta fi daya. Kuma ma a wannan zamani, duk wani wanda ya ke da halin ya kara kamar M. Sadiq, bai kamata ya yi kasa a gwiwa ba, duba da yawaitar ‘yan mata maras aure da suka yawaita a kasar Hausa.
Ga hotunan ango da amarya:







Allah ya kawo na yan gaba

No comments:

Post a Comment